Gwamnatin Buhari za ta binciki kamfanin Cambridge Analytica

Asalin hoton, Facebook/Buhari Sallau
Marigayi Umaru 'Yar Adu ne ya lashe zaben shekarar 2007, yayin da Muhammadu Buhari ya zo na biyu
Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti da zai binciki kamfanin Cambridge Analytica kan ko ya yi katsalandan a zabukan shekarar 2007 da 2015, kamar yadda fadar shugaban kasar ta bayyana.
Cambridge Analytica, wanda yake tattara bayanai kan zabuka, ya tsinci kansa a cikin ce-ce-ku-ce saboda ikirarin da aka yi cewa ya yi amfani da bayanan miliyoyin masu amfani da shafin Facebook domin cimma burin siyasa a kasashen Amurka da Birtaniya.
Mai taimakawa shugaban Najeriya kan yada labarai Malam Garba Shehu ya ce "kwamitin zai fara duba irin rahotannin da aka samu kan cewa kamfanin ya hada kai da tsohuwar gwamnatin Najeriya domin karya dokokin zabe."
Kamfanin dai bai ce uffan ba tukuna game da zargin yin katsalandar a zabukan Najeriya.
Ya ce ana zargin kamfanin ya rika duba sakon i-mel na muhimman mutane a Najeriya ciki har da na Shugaba Muhammadu Buhari lokacin da yake neman shugabancin kasar.
Hakazalika ya yi zargin cewa an yi amfani da kamfanin wajen yin "batanci ga wadansu 'yan Najeriya don kada su samu nasara a zabe."
- Latsa alamar lasifika da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar da BBC ta yi da Malam Garba Shehu
Hirar BBC da Garba Shehu
Har ila yau, kwamitin zai duba ko kamfanin ya saba doka game da aikin kwangilar da ya yi wa jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya.
Sai dai ba a bayyana lokacin da ake saran kwamitin zai kammala aikin binciken ba, da kuma matakan da za a dauka idan aka same shi da laifi.