An sace amarya da 'yan rakiyarta a jihar Kaduna

Amarya

Asalin hoton, Getty Images

Ana ci gaba da alhinin sace wata amarya a kan hanyarta ta zuwa gidan miji a yankin karamar hukumar Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Ana zargin masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa ne suka sace amaryar, mai suna Halima, tare da masu yi mata rakiya lokacin da hanya ta biyo da su jihar a kan hanyarsu ta zuwa jihar Neja daga jihar Katsina, bayan an daura aure.

Angon ya shaida wa BBC cewa, sun je daurin aure ne a karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina daga karamar hukumar Hushishi a jihar Neja.

Ya ce an kamma biki lafiya, to amma wurin dawowa a ranar Asabar bayan an daura aure sai muka kama hanyar koma wa jihar Neja da amaryar.

"Mun isa yankin Birnin Gwari ne da marece kuma a lokacin daya daga cikin direbobin motar da ke dauke da amaryar ya fada hannun masu garkuwa da mutanen".

Daga nan ne sai masu satar mutanen suka tisa keyar amaryar da sauran 'yan uwanta da ke mata rakiya, kamar yadda angon ya bayyana.

  • Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar BBC da angon
Bayanan sauti

Muryar angon da aka sace wa amarya a Kaduna

Har yanzu amaryar na ci gaba da kasancewa hannun masu garkuwa da mutanen, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Sai dai rundunar 'yan sanda a jihar ta ce ba za ta ce komai ba game da batun sa ce amaryar, har sai ta samu gamsassun bayanai.

Wannan batun na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake cewa an yi sulhu da masu satar mutane a yankin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.