Amitabh Bachchan zai fito mai shekara 102 a fim

Asalin hoton, TIMOTHY A. CLARY
Amitabh ya kware wajen fitowa a fina-finan barkwanci
Shahararren jarumin fina-finan Indiya Amitabh Bachchan, zai fito a matayin mahaifin Rishi Kapoor a wani sabon fim, mai suna "102 Not Out".
Jarumi Amitabh da Rishi Kapoor, za su fito a fim ne tare bayan kwashe shekaru da dama ba a gansu a cikin fim guda ba.
Daraktan fim din, Umesh Shukla, ya ce lokacin da aka yi wa kowanne daga cikinsu tayin fitowa a fim din ba su ba ta lokaci ba suka amince da bukatar.
Fim din mai suna "102 Not Out", fim ne na barkwanci wanda ya kunshi labarin da da uba.
Amitabh Bachchan zai fito a matsayin dattijo ne mai kimanin shekara 102 wanda yake da haba-haba da mutane ,yayin da shi kuma Rishi Kapoor, zai fito mai shekara 75 a fim din zai fito a matsayin dansa marar azanci.
Daraktan fim din ya ce ya jima yana nazari a kan wadanda za su taka wannan rawa ta da da uba da za ta dace.
Taken fim din shi ne "Uba dan kwalisa, da kuma cus".
Asalin hoton, Indian express
Amita Bachchan da Rishi Kapoor
Fim din na ba da labarin wani dattijo ne mai shekara 102 (Amitabh Bachchan) wanda yake so ya kafa sabon tarihin kasancewa mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya — a halin da ake ciki a fim din kuwa wanda ya fi kowa tsufa wani dan China ne mai shekara 118.
Dattijo wato Amitabh Bachchan, ya shirya yin hakan ne kuma ta hanyar kai dansa mai shekara 75 gidan kula da tsofaffi.
Kamar yadda tallan fim din ya nuna dai, "102 Not Out" ya yi hannun riga sosai da batutuwan da sauran fina-finan Indiya suka fi mayar da hankali a kai, wato soyayya da barkwanci.
Jama'a da dama a kasar da sauran kasashe sun zaku da fitowar wannan fim din, kasancewar an jima ba a ga jaruman sun fito a cikin fim tare da ba.
Fim din Naseeb, shi ne fim na karshe da suka fito a tare, wato kusan shekara 27 ke nan.
Fina-finan da Amitabh da Rishi suka fito tare
- Kabhie Kabhie
- Amar Akbar Anthony
- Coolie
- Ajooba
- Naseeb
Za dai a saki fim din wato "102 Not Out" a ranar 4 ga watan Mayu mai zuwa.