Ko kun san jaruman India masu karancin ilimin boko?
Hausawa kan ce ilimi gishirin rayuwa, kuma ilimi na taka muhimmiyar rawa a rayuwar bil'adama.
Idan muka duba yadda fina-finan Bollywood da ma jaruman cikinsu suka yi suna a duniya, za mu yi mamaki idan aka ce akwai wasunsu da ba su yi nisa a karatu ba.
Wasu daga cikinsu dai sun ajiye karatun ne saboda burin da ke cikin ransu na son zama jarumai.
Ga wasu daga cikin jaruman na Bollywood da ke da karancin ilimi.
1. Salman Khan
Asalin hoton, Getty Images
Salman Khan ya fito a fina-finai sama da 100
Salman Khan, ya fara karatunsa ne daga makarantar St. Stanislaus High School da ke Bandra, a birnin Mumbai.
Daga nan sai ya wuce zuwa kwalejin Elphinstone, amma a shekararsa ta biyu da fara karatun sai ya bari.
2. Katrina Kaif
Asalin hoton, Getty Images
Katrina Kaif na daga cikin matan da suka fi daukar albashi mai tsoka a Bollywood
Katrina ta rinka yawo tsakanin wannan birni da wancan inda daga nan sai ta shiga sana'ar tallata kayan kawa wato modelling a Turance, a lokacin da ta ke kan kuruciyarta.
Saboda wannan dalili ba ta samu damar kammala karatunta ba.
3. Akshay Kumar
Asalin hoton, Getty Images
Akshay Kumar yana da takardar zama dan kasar Kanada
Akshay Kumar ya fara karatunsa ne daga makarantar Don Bosco, daga nan sai ya ci gaba a kwalejin Guru Nanak Khalsa da ke Mumbai, amma daga bisani bayan shekara guda da farawa, sai ya dai na zuwa.
Dag nan ne kuma Akshay ya tafi Bangkok domin koyan wasan fada da kare kai.
4. Deepika Padukone
Asalin hoton, Getty Images
Deepika Padikone ta lashe kyaututtuka da dama a fagen fim
Deepika ta yi karatu a Sophia High School da ke Bangalore inda ta kammala karatun share fagen shiga jami'a a kwalejin Mount Carmel.
Daga na sai ta wuce zuwa jami'ar karatu daga gida ta Indira Gandhi inda ta fara karatun digiri a fannin ilimin sanin zaman takewar dan adam.
Amma daga bisani ta yanke saboda yanayin tsarin sana'arta da ta sanya a gaba ta tallan nuna kayan kawa wato modelling.
5. Ranbir Kapoor
Asalin hoton, Getty Images
Ranbir Kapoor na cikin fitattun jaruman India
Ranbir ya yi karatunsa ne a Bombay Scottish School da ke Mahim.
Ya kasance bashi da sha'awar karatu hakan ya sa ya zamo koma baya a cikin abokan karatunsa.
6. Kajol
Asalin hoton, Getty Images
Kajol diya ce ga jarumi Tanuja Samarth da kuma mai shirya fina-finai Shomu Mukherjee
Kajol ta yi karatu a makarantar kwana ta St Joseph Convent da ke Panchgani.
Tana 'yar shekara 16 ne ta fara fim, inda ta fito a fim din Bekhudi, na Rahul Rawail.
Da farko ta yi niyyar ci gaba da karatunta bayan kammala shirin fim din, to amma daga baya hakan bai samu ba, sai ta mayar da hankalinta a kan fitowa a fina-finai.
7. Aamir Khan
Asalin hoton, Getty Images
Aamir Khan na daya daga cikin jaruman da suka fi magoya baya a India
Aamir Khan ya fara karatunsa ne a J.B. Petit School, daga nan ya wuce St. Anne's High School da ke Bandra. Daga bisani ya wuce Bombay Scottish School da ke Mahim.
A lokacin da ya ke a babbar makarantar, ya kasance mai buga wasan kwallon Tennis inda har ma ya yi fice.
Ba a nan kawai ya tsaya ba, Aamir Khan ya iya buga wasan kwallon kafa sosai a lokacin da ya ke makaranta, don har suna ya yi a kan wasan.
Ya dai kammala karatunsa na kwaleji, amma daga nan bai je jami'a ba.
8. Aishwarya Rai
Asalin hoton, Getty Images
An taba zabar Aishwarya Rai sarauniyar kyau a shekarar 1994
Aishwarya ta fara karatu ne a Arya Vidya Mandir High School, daga nan ta wuce kwalejin Jai Hind, ba ta karasa ba sai aka canza mata makaranta ta koma kwalejin DG Ruparel da ke Matunga.
Ta samu horo a bangaren rawa na tsawon shekara biyar a lokacin ba ta fi shekara 10 ba.
Da farko ta so ta karanci aikin likita, amma daga bisani sai ta canja zuwa karatun koyan zane-zane wato Architecture.
Ta fara wannan karatu a kwalejin Raheja, amma daga baya sai ta daina zuwa ta mayar da hankali a kan sana'arta ta tallan kayan kawa.
9. Prateik Babbar
Asalin hoton, Getty Images
Prateik Babbar na cikin matasan jaruman Bollywood
Prateik ya fara karatu ne daga AVM Bandra, daga nan sai ya koma kwalejin Jai Hind, sannan ya wuce zuwa kwalejin St. Andrew.
Sai da ya yi rabi a karatu a kwalejin sai kawai ya dai na zuwa.
10. Sridevi
Asalin hoton, Getty Images
Sridevi ta rasu a ranar 24 ga watan Fabrairun bana a Dubai
Sridevi ta fara fim ne tun tana yarinya, daga nan har ta girma.
Wannan ne dai dalilin da ya sa ake ta jita-jita a kan cewa ba ta yi karatu ba, saboda fim da ta rinka yi tun tana yarinya.