Ibada da fim ne suka fi muhimmanci a wurina -– Jamila Nagudu

Shahararriyar 'yar wasan Kannywood, Jamila Nagudu, ta shaida wa BBC cewa babu sa'arta a duk matan da suke harkar fim a yanzu - a don haka ita uwa ce.

A hirarta da Yusuf Yakasai a Kano, 'yar fim din ta ce kwarewa ce ta sa ta ke iya taka kowacce rawa da aka nemi ta yi a fim.