Fafaroma ya sa wa dan Najeriya albarka

Fafaroma na yi wa John Ogah baftisma
Bayanan hoto,

Fafaroma na yi wa John Ogah baftisma

Fafaroma Francis ya yi wa wani dan Najeriya mai suna John Ogah baftisma ana gobe Easter.

Shi dai John ya tafi Italiya ne a matsayin bakon haure, amma sai kuma ya zamo wani gwarzo bayan ya kama wani barawo mai dauke da adda.

Jarumtar da ya nuna ta sa 'yan sanda sun bashi lambar yabo kuma suka taimaka masa ya samu izinin zama a kasar.

John ya bayyana yadda ya ji da baftisman da aka yi masa:

"A ce Fafaroma ne yayi maka baftisma, hakan na nufi babbar makoma da albarka."

Ya kar da cewa, "A da ni ba kowa ba ne amma a yanzu na zama wani abu. Fafaroma ya dora hannunsa a kaina, wannan ya akara tabbatar min da cewa ni wani ne."

A ranar 10 ga watan Mayu 2014 ne John ya je Italiya, kuma ya shekara biyu yana neman a ba shi izinin zama a kasar, amma sai aka sanar da shi cewa an ki amincewa da bukatarsa.

A takaice an yi watsi da bukatarsa ta neman zama a Italiya.

"Sau biyu kenan, kuma sai na zamo na rasa abin yi. Kuma hakan ya sakani cikin wani mawuyacin hali."

Bayanan hoto,

John Ogah a lokacin da Fafaroma ya yi masa baftisma

Yadda ya zama jarumi

A watan Satumbar 2017, John na tsaye a gaba wani shago sai ya ga wani mutum ya tsaya da babur.

Mutumin ya umarce shi da ya bar wurin, amma John bai motsa ba inda ya tambaye hi dalilin da yasa ya ce ya bar wurin.

Sai mutumin ya sanar da shi cewa shi barawo ne.

"Na yi tsammanin wasa yake yi, saboda haka sai na koma wurin da nake zama."

John ya kara da cewa: "Sai naga ya fito da wata katuwar wuka daga jakarsa, kuma ya shiga cikin shagon yana cewa su ba shi cinikinsu na wannan ranar."

Barawon ya sami karbar kudi kimanin euro 400.

A lokacin ne John ya shiga shagon inda ya fara kokwa da mutumin duk da yake yana rike da katuwar wuka.

Ya yi nasarar kwace wukar daga hannun barawaon kuma ya rike hi har sai da 'yan sanda suka isa wurin.

"Abin da yayi ba abu ne mai kyau, domin a cikin littafin Babul an ce kada ka yi sata - a shirye na ke in sake hana wani idan da hakan zai sake faruwa."

A sanadiyyar wannan jaruntar da ya nuna, jami'an 'yan sanda sun taimaka masa an ba shi izinin zama a kasar.

A halin yanzu yana aiki da kungiya Red Cross.