Cutar zazzabi Lassa ta kashe wata likita a jihar Abia

Zazabin Lassa na kara yaduwa a Najeriya
Bayanan hoto,

Cutar zazzabi Lassa na da matukar hadari ga rayuwar likitoci

Labarin mutuwar wata matashiyar likita ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafan sada zumuntar Najeriya.

Likitar wadda ke neman kwarewar aiki ta mutu ne sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa, a wani asibitin koyarwa da ke Umuahia, babban birnin jihar Abia da ke gabashin Najeriyar.

Yanzu haka dai kasar na tsakiyar fama da bullar cutar wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 90, ciki har da jami'an lafiya.

Wata likita ta rubuta a shafinta na sada zumunta cewa, ba za ta ci gaba da sanya rayuwarta cikin hadari ba, matukar gwamnati ba ta samar da kayayyakin aikin da ya kamata a rinka kula da wadanda suka kamu da cutar ba a asibitoci.

Dr Adebayo Sekunmade, shi ne shugaban kungiyar likitoci masu neman kwarewar aiki a asibitin koyarwa na jami'ar Lagos, ya ce, kayayyakin aikin da ake bukata ba a samunsu.

Dr Adebayo ya shaida wa sashen BBC na turancin Buroka cewa, "Kasancewar alawus din da ake biya don shiga hadari bai taka kara ya karya ba, ba abu ne da zai karfafa gwiwar likitoci su sadaukar da kansu domin marasa lafiya ba".

A saboda haka, " Ina ga ya kamata likitoci su rinka sara suna duban bakin gatari kafin su duba marassar lafiyar da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, da ma sauran cutukan da suke da matukar hadari".

To sai dai kuma, shugaban asibitin da likitar ta mutu ya ce, suna da kayayyakin aikin da suka dace, inda ya ce, wannan shi ne karon farko da aka samu wanda ya mutu sakamakon cutar Lassa a asibitin.

Shugaban asibitin ya ce " Muna bin matakan kariya wanda aka amince da shi a duniya baki daya, sannan kuma zamu sake duba yanayin asibitin ta fuskar kayayyakin aikin da ake da su, sannan kuma mu sake inganta su".

Likitan ya ci gaba da cewa, " Ba bu wanda zai tabbatar da cewa likitar ta kamu da cutar ne daga asibitinmu, kuma idan hakan ma ta yi wu, zamu iya cewa lallai akwai wani abu da ya faru".

Karin bayani a kan cutar zazzabin Lassa

  • Kwayar cutar na yaduwa ne ta hanyar tu'ammali da abinci da kuma kayayyakin amfanin gida da suka gurbata da fitsari da kashin bera ko kuma ta hanyar shafar duk wani ruwa-ruwa daga jikin mutum da ya kamu.
  • Lassa na da kamanceceniya da cutukan Ebola da Marburg inda yake haddasa zazzabi da haraswa da idan kuma ya yi tsanani sai maras lafiya ya fara zubar da jini.
  • Ana ta samun karuwar yaduwar zazzabin cutar Lassa a fadin Najeriya.
  • Shan garin kwaki ma yana kawo kamuwa da cutar zazzabin Lassa