Mace ta kori zaki da sanda don ya kai wa akuyarta hari

Rupali a lokacin da ta shiga gida bayan fada da zaki Hakkin mallakar hoto RUPALI MESHRAM
Image caption Rupali a lokacin da ta shiga gida bayan fada da zaki

Wata matashiya a India ta tsallake rijiya da baya, bayan ta kori wani zaki da sanda saboda ya kai wa akuyarta hari.

Rupali Meshram, 'yar shekara 23 da haihuwa, ta ce bayan da ta ji akuyar ta na ihu, sai ta yi maza ta ruga ta nufi inda akuyar ta ke a wajen gidansu.

Daga nan ne sai ta dauki sanda ta fara dukan zakin, wanda daga baya kuma ya afka mata.

Mahaifiyarta wadda ita ma ta samu raunuka, ita ta ce-ce ta ta hanyar ingizata cikin gida.

Dukkanninsu dai sun samu raunuka, amma ya zuwa yanzu an sallame su daga asibiti, sai dai kuma akuyar ba ta rayu ba.

Hakkin mallakar hoto SANJAY TIWARI
Image caption Rupali da mahaifiyarta bayan ta sun samu sauki

Rupali ta dauki hoton selfie jim kadan da faruwar lamarin a makon da ya wuce a yammacin jihar Maharashtra, fuskarta duk jini.

Likitan da ya dubata ya yaba mata sosai, inda ya ce, ta yi namijin kokari da ta tunkari zakin, amma kuma ta yi babbar sa'a da zakin bai cije ta ba.

Matashiyar dai ta samu raunuka a kanta da kwankwasonta da hannunta, amma ta na samun sauki sosai.

Sannan kuma ta bayyana alhininta na rasa akuyarta.

Mahaifiyar Rupali ta shaida wa BBC cewa, " Na zaci 'ya ta za ta mutu saboda yadda naga ta na kokarin ceton kanta da sanda daga hannun zakin da kuma irin jinin da naga ya na zuba daga jikinta".

Kauyen su Rupali dai na kusa da wani daji ne, kuma yana fuskantar barazanar shigar namun daji a kai-a kai.

Don haka suke kira ga masu kula da namun dajin da ke kusa da kauyen na su, da su rinka sa ido a kan dabbobin saboda gudun faruwar wani lamari kamar na Rupali.

Labarai masu alaka