Na kadu da rasuwar Sanata Bukar - Buhari

Sanata Mustapha Bukar
Bayanan hoto,

Sanata Bukar yana da kusanci da Shugaba Muhammadu Buhari

Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Daura a jihar Katsina, Mustapha Bukar, ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, kamar yadda iyalansa suka bayyana.

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana a Twitter cewa "Marigayin ya ba da gudunmuwa sosai yayin da ake tattauna muhimman babutuwa a zauren majalisar".

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda suka fito daga mazaba daya da sanatan, ya ce ya kadu da mutuwarsa yana mai cewa "babban rashi ne" ga al'ummar kasar.

Zuwa yanzu babu wani bayani da aka samu kan musabbabin rasuwar dan majalisa, wanda ya rasu yana da shekara 64.

Marigayin wanda injiniya ne, an haife shi ne a garin Daura a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 1954.

A cikin watan jiya ne wani sanata daga jihar Bauchi, Ali Wakili, ya rasu - a wani lamari da ya kada da dama daga cikin 'yan siyasar kasar.

Hakazalika a makon jiya ne mataimakin shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan kasar Umar Baba Jibril daga jihar Kogi, ya rasu bayan wata gajeriyar rashin lafiya a Abuja.

Bayanan hoto,

Marigayi Sanata Ali Wakili ne shugaban kwamitin yaki da talauci na majalisar dattawan Najeriya

Alhini

Jam'iyyar APC mai mulkin kasar, wanda marigayin danta ne, ta ce mutuwar Sanata Bukar wani babban rashi ne ga jam'iyyar, kamar yadda babban sakataren jam'iyyar Malam Bolaji Abdullahi ya bayyana.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce marigayin ya taka rawa tun yana matashin injiniya wurin kawar da matsalar ruwan sha da ta addabi jihar Katsina.

"A kodayaushe na kan kadu da mutuwar gwarazon 'yan Najeriya masu hazaka irin su Sanata Bukar," a cewar wata sanarwa da ofishinsa ya fitar.

Shi ma shugaban majalisar dattawan kasar Sanata Bukola Saraki, ya jinjina wa marigayin:

"... Ina fatan Allah ya jikan marigayi Sanata Bukar ya kuma saka masa da Aljannah".

"Na kadu matuka da jin labarin rasuwar Sanata Bukar. Duk da cewa wannan ne karonsa na farko da ya zo majalisa, ya yi fice wurin bayar da gudummawa sosai a muhawar da ake yi a zauren majalisar".

Shi ma shugaban majalisar wakilai ta kasar Yakubu Dogara, ya ce ya kadu da jin labarin rasuwar marigayin:

"... Mutum ne mai tsayawa kan gaskiya kuma ina fatan Allah ya bai wa iyalansa da sauran makusantansa ikon jurewa wannan rashi".