Najeriya: 'Yan majalisar kasa nawa ne suka mutu kwanan nan?

  • Raliya Zubairu
  • BBC Abuja
Sanata Mustapha Bukar

Asalin hoton, Facebook

Bayanan hoto,

An haifi Sanata Mustapha Bukar a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 1954

Rasuwar Senata Mustapha Bukar ita ce ta baya-bayanan a cikin jerin 'yan majalisun dokoki da suka rasu a Najeriya. A baya dai ba kasafai manyan 'yan siyasar ke rasuwa ajere-ajere ba kamar haka, abin da ya sa lamarin ke ci gaba da daukar hankalin jama'a a kasar.

Sanatan mai wakiltar mazabar Daura a jihar Katsina ya rasu ne da safiyar ranar Laraba ,kamar yadda iyalinsa suka bayyana.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda suka fito daga mazaba daya da sanatan, ya ce ya kadu da mutuwarsa yana mai cewa "babban rashi ne" ga al'ummar kasar.

Zuwa yanzu babu wani bayani da aka samu kan musabbabin rasuwar dan majalisa, wanda ya rasu yana da shekara 64.

Marigayin wanda injiniya ne, an haife shi ne a garin Daura a ranar 31 ga watan Disambar shekarar 1954.

Mun yi waiwaye kan wasu daga cikin 'yan majalisar da suka rasu a baya-bayan nan:

Sanata Ali Wakili

Asalin hoton, Nigerian Senate

Bayanan hoto,

Marigayi Sanata Ali Wakili ne shugaban kwamitin yaki da talauci na majalisar dattawan Najeriya

A ranar 17 ga watan Maris Sanata Ali Wakil da ke wakiltar mazabar Bauchi ta kudu a majalisar dattawan Najeriya ya rasu.

Marigayin ya rasu yana da shekara 58 a duniya.

Babu wani bayani da aka samu dai kan musabbabin rasuwar marigayin, sai dai an yi ta yadawa a kafafen sadarwa na zamani cewa kwana daya kafin ya rasu ya halarci daurin auren diyar Aliko Dangote, wanda ya fi kowa kudi a Afirka, da aka yi a Kano.

Wane ne Sanata Ali Wakili?

  • An haife shi a shekarar 1960, ya mutu yana da shekara 58
  • Dan asalin karamar hukumar Tafawa Balewa ne a jihar Bauchi
  • Ya kammala digirinsa a Jami'ar Bayero da ke Kano a 1982
  • Ya dade yana aiki a Hukumar Hana Fasa Kwauri ta Najeriya tun daga 1984
  • Ya zama sanata mai wakiltar Bauchi Ta Kudu a 2015
  • Shi ne shugaban kwamitin Yaki da Talauci na majalisar dattawa
  • Ya rasu ranar 17 ga watan Maris na 2018
  • Ya bar mata biyu da 'ya'ya 10.

Bayanai: Daga Majalisar Dattawa da iyalinsa

Hon Umar Buba

Asalin hoton, NAtional assembly

Bayanan hoto,

Yakubu Dogara ya bayyana Hon Umar Buba da cewa 'kwararren dan majalisa ne'

Hon Umar Buba Jibril da ke wakiltar mazabar Lokoja da ke jihar Kogi a majlisar wakilan Najeriya ya rasu a karshen watan Maris yana da shekara 58 a duniya.

Kafin ya rasu shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan ta kasa.

Ya kuma taba zama kakakin majalisar dokoki ta jihar Kogi.

Kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara ya bayyana shi a matsayin mutumin da ba ya kunbiya-kunbiya, mai kishin kasa, wanda kuma yake da kwarewar shugabanci.

Asalin hoton, Majalisar Wakilai

Bayanan hoto,

Shugaban Majalisar Wakilai Yakubu Dogara tare da Sanata Dino Melaye lokacin da suka kai ziyarar ta'aziyya gidan wani dan majalisar wakilai,Umar Baba Jibril daga jihar Kogi, wanda ya rasu ranar Juma'a a gidansa da ke Abuja.

Dogara ya kara da cewa Hon Jibril yana aiki tukuru kuma ya cancanci wakiltar jama'arsa.

Shugaban majalisar ya kuma yi alhini kan yadda abokan aikinsa da dama suka rigamu gidan gaskiya a baya-bayan nan.

Sai dai ya ce haka mahalicci ya tsara kuma kowanne dan'adam zai bar duniya.

Hon Independence Ogunewe

Asalin hoton, facebook

Bayanan hoto,

Hon Independence Ogunewe ya zauna a majalisa daga 2003 zuwa 2011

A ranar Talata ne tsohon dan Majalisar wakilai da ke wakiltar mazabar Ahiazu da Ezinihitte a jihar Imo a Maalisar wakilai ta kasa shi ma ya rasu.

Ya mutu yana da shekara 57 a duniya.

Rahotanni sun ce ya mutu ne a gidansa da ke Abuja kuma kawo yanzu babu masaniya kan musabbabin mutuwar tasa.

Ya wakilci jama'ar mazabarsa daga shekara ta 2003 zuwa 2011.

An haife Hon Ogunewe a birnin Warri a ranar 22 ga watan Afrilu na 1960.

Hon Bello Sani

Asalin hoton, Dailytrust

Bayanan hoto,

Hon Bello Sani ya taba zama shugaban karamar hukuma a Katsina

Hon Bello Sani da ke wakiltar mazabar Mashi da Dutsi a jihar Katsina a majlisar wakilan Nijeriya ya rasu a ranar 15 ga watan Fabrairu.

Ya rasu yana da shekara 51 da haihuwa a duniya.

Ya taba zama shugaban Karamar Hukumar Mashi a jihar ta Katsina.

Sannan an ta ba zamarsa wakili a majalisar dokoki ta jihar Katsina.

A lokacin da ya rasu, Kakakin Majalisar Yakubu Dogara ya bayyana shi a matsayin mutum mai faran-faran da jama'a kuma mai aiki tukuru.