Sanata mai wakiltar Daura ya rasu, An tura dakaru na musamman Zamfara
Sanata mai wakiltar Daura ya rasu
Dan majalisar dattawa mai wakiltar mazabar Daura a jihar Katsina, Mustapha Bukar, ya rasu ne a safiyar ranar Laraba, kamar yadda iyalansa suka bayyana.
Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya bayyana a Twitter cewa "Marigayin ya ba da gudunmuwa sosai yayin da ake tattauna muhimman babutuwa a zauren majalisar".
Asalin hoton, Facebook
Sanata Bukar yana da kusanci da Shugaba Muhammadu Buhari
An tura dakaru na musamman Zamfara
Rundunar sojin sama ta Najeriya ta ce ta aike da dakaru na musamman zuwa Gusau babban birnin jihar Zamfara.
Rundunar ta ce an dauki wannan mataki ne a kokarin da jami'an tsaro ke yi na dakile ayyukan barayin shanu masu hallaka jama'a.
Asalin hoton, Nigerian Air Force
Dakarun yayin da suke shirin isa jihar ranar Talata
Cutar Lassa ta kashe likita a Najeriya
Labarin mutuwar wata matashiyar likita ya janyo ce-ce-ku-ce a kafafan sada zumuntar Najeriya.
Likitar wadda ke neman kwarewar aiki ta mutu ne sakamakon kamuwa da cutar zazzabin Lassa, a wani asibitin koyarwa da ke Umuahia, babban birnin jihar Abia da ke gabashin Najeriyar.
Asalin hoton, SANJAY KANOJIA
Cutar zazzabi Lassa na da matukar hadari ga rayuwar likitoci
Mace ta kori zaki da sanda don kare akuyarta
Wata matashiya a India ta tsallake rijiya da baya, bayan ta kori wani zaki da sanda saboda ya kai wa akuyarta hari.
Rupali Meshram, 'yar shekara 23 da haihuwa, ta ce bayan da ta ji akuyar ta na ihu, sai ta yi maza ta ruga ta nufi inda akuyar ta ke a wajen gidansu.
Asalin hoton, RUPALI MESHRAM
Rupali a lokacin da ta shiga gida bayan fada da zaki
Kungiyar 'yan uwa Musulmi wadda aka fi sani da Shi'a ta bukaci gwamnatin Najeriya ta saki shugabansu Sheikh Ibrahim el-Zakzaky, yayin wata zanga-zanga da suka yi a Abuja ranar Laraba.
Fiye da shekara biyu ke nan gwamnatin Najeriya tana rike da jagoran kungiyar.
Asalin hoton, WhatApp/Saminu
Asalin hoton, WhatsApp/Saminu
Bidiyo: 'Ibada da fim ne suka fi muhimmanci a wurina'
Abin da ya sa nake taka kowacce rawa a fim – Jamila Nagudu
Karanta karin wasu labaran
Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.