Julius Maada Bio: An rantsar da sabon shugaban Saliyo a otel

Julius Maada Bio yana shan rantsuwa
Bayanan hoto,

Julius Maada Bio ya taba shugabantar kasar na wani dan lokaci a baya

An rantsar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a kasar Saliyo, Julius Maada Bio a otal, bayan ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da aka gudanar.

Mista Maada Bio tsohon shugaban mulkin sojin kasar ne wanda ya yi mulki na wani dan takaitaccen lokaci a shekarar 1996.

Ya doke dan takarar jam'iyya mai mulki Samura Kamara, wanda ya yi zargin an tafka magudi sannan ya ce zai kalubalanci sakamakon a kotu.

An rantsar da Mista Bio ne ranar Laraba, kasa da sa'a biyu bayan sanar da sakamakon zaben na ranar Asabar.

Ya ce "[Wannan wani] sabon zamani ne muka shiga". "Mutanen wannan kasa sun zabi bin wani sabon tafarki."

A wani jawabi ta gidan talabijin, Mista Kamara ya ce "Ba mu amince da sakamakon zaben ba kuma za mu dauki matakin shari'a domin kawo gyara."

Sannan ya bukaci magoya bayansa da su kwantar da hankulansu.

Mista Maada Bio, wanda shi ne shugaban jam'iyyar Sierra Leone People's Party (SLPP), ya samu nasara ne da kasa da kashi 52 cikin 100 na kuri'un da a kada.

Bayanan hoto,

Tsohon Shugaba Koroma (dama) yana kamfe tare da Mista Samura Kamara (hagu)

Wa zai gada?

Shugaba mai barin gado, Ernest Bai Koroma, ya sauka bayan da ya kammala wa'adi biyu na shekara biyar-biyar a karkashin jam'iyyar All People's Congress (APC).

Shi ne ya zabi Mista Kamara domin ya maye gurbinsa.

Mista Maada Bio ya sha kaye a zaben farko na zaben a hannun Mista Komora.

Kabilanci yana da tasiri a goyon bayan da jam'iyyun biyu ke da shi.

SLPP, wacce ita ce jam'iyya mafi dadewa a kasar, ta fi farin jini a kudanci da kuma gabashin kasar.