Za a bude gidan sinima na farko a Saudiyya

Saudi women attend a short-film festival in Riyadh on 20 October 2017

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Matan Saudiyya na yawan kallon fina-finan kasashen Yamma - amma yawanci a sirri suke yin hakan

A karon farko cikin shekara 35 za a bude gidan sinima na farko a kasar Saudiyya a ranar 18 ga watan Afrilu.

Abin da zai share fagen bude wadansu gidajen sinimar kusan 100 a fadin kasar nan da shekarar 2030.

A baya dai a shekarun 1970 akwai gidajen sinima, a kasar, amma kuma aka rufe su saboda maganganu da tasirin malaman addinin Musulunci da ke daular.

Tun bayan da hukumomin Saudiyyar suka sanar kimanin watanni hudu da suka gabata cewa za a sake bude gidajen sinima a kasar bayan kusan shekara 40 da rufe su, abubuwa sun gudana cikin gaggawa na tabbatar wannan alkawari.

Ranar 18 ga wannan wata na Afrilu, ita ce Saudiyyar ta sa domin bude kofar sinimar ta farko a babban birnin kasar, Riyadh.

Hakan na daga yarjejeniyar da kasar ta kulla da babban kamfanin gidajen sinima na duniya AMC, inda a karkashin shirin zai bude gidajen sinima 40 a biranen Saudiyyar daban-daban a cikin shekara biyar nan gaba.

Wata mace a Saudiyya

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An yi wani bikin bajakolin fina-finai a Riyadh a watan da ya gabata

A shekarar data wuce hukumomin na Saudiyya sun dukufa sosai wajen shigar da harkoki nishadi kasar, a matsayin wani muhimmin mataki na bunkasa kasar nan da shekara ta 2030, mai taken Vision 2030.

Wato shirin aiwatar da sauye-sauye na tattalin arziki da zamantakewa wanda Yarima mai-jiran-gado Mohammed Bin Salman, wanda yanzu yake Amurka wajen gayyato masu zuba jari a kasar, ya bullo da shi.

Shiri ne wanda kasar ta bullo da shi domin fadada tattalin arzikinta ta yadda za ta kauce daga dogaro da mai, tare da samar da sabbin ayyuka da kuma samar da hanyoyin da 'yan kasar za su rika zama suna kashe kudadensu a gida, maimakon fita kasashen waje.

Ana sa ran zuwa shekara ta 2030 za a samu gidajen sinima kusan 100 a kasar, wanda wannan shiri ne da zai kasance wani abin maraba ga 'yan kasar da ke da sha'awar zuwa gidajen sinima.