PDP na goyon bayan sauya tsarin zabe

Lema ita ce alamar jam'iyyar PDP

Asalin hoton, PDP

Bayanan hoto,

PDP ta ce babban burinta shi ne ta sake fafata wa da Shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP na goyon bayan sauya tsarin zabe da Majalisar Dokoki ta kasar ta yi, kamar yadda mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Babayo Garba Gamawa ya ce.

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Bauchi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwato, Sanata Gamawa ya ce, a matsayin PDP na jam'iyya mai bin doka za ta mutunta matsayin Majalisar Tarayyar saboda 'yan majalisar na wakiltar mafi yawan 'yan Najeriya.

Tsohon dan majalisar dattawan ya ce 'yan Najeriya a yau suna fuskantar kalubale da wahalhalu a karkashin gwamnatin APC, fiye da a baya, kamar yadda ake gani a yawan fatara da yunwa da cutuka da kuma tsadar rayuwa a kasar.

Mataimakin shugaban na PDP ya kuma ce yanayin rayuwa talakan Najeriya ya fi a lokacin mulkin PDP, yana mai zargin cewa APC ta gaza wajen cika alkawuranta na yakin neman zabe.

Ya sha alwashin cewa PDP za ta dawo mulki ta kuma inganta rayuwar 'yan Najeriya ta hanyar tsare-tsare masu amfani ga jama'a.

Wannan layi ne

Bayani kan sabuwar dokar zaben

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Muhammadu Buhari ne dan adawa na farko da ya lashe zabe a Najeriya

  • Za a fara ne da zaben 'yan majalisa tarayya
  • Daga nan sai zaben gwamnoni da 'yan majalisar jihar
  • Sai a karshe a yi zaben shugaban kasa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ki sanya hannu a daftarin sabuwar dokar da majalisar ta aika masa.

Ga alama shugaban ya fi so a ci gaba tsarin fara zaben shugaban kasa a farko, maimakon a kai shi karshe.

Sai dai 'yan majalisar za su iya zama game da batun kuma idan kudirin ya samu goyon bayan kaso biyu cikin uku na 'yan majalisa, ya zama doka.