Za a rataye mutumin da ya saci giya a Najeriya, An rantsar da sabon shugaban Saliyo a otel

Salman Khan zai yi shekara biyar a gidan yari

Wata kotu a kasar India ta yankewa jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar saboda ya yi farautar gwanki da ba kasafai ake samunta ba ba bisa ka'ida ba.

Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154.

Bayanan hoto,

Salman Khan zai zauna gidan yari na wani lokaci

PDP na goyon bayan sauya tsarin zabe

Babbar jam'iyyar hamayya a Najeriya, PDP na goyon bayan sauya tsarin zabe da Majalisar Dokoki ta kasar ta yi, kamar yadda mataimakin shugaban jam'iyyar na kasa Sanata Babayo Garba Gamawa ya ce.

A wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Bauchi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwato, Sanata Gamawa ya ce, a matsayin PDP na jam'iyya mai bin doka za ta mutunta matsayin Majalisar Tarayyar don 'yan majalisar na wakiltar mafi yawan 'yan Najeriya.

Bayanan hoto,

PDP ta ce babban burinta shi ne ta sake fafata wa da shugaba Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019.

'Yan majalisar kasa nawa ne suka mutu kwanan nan?

Mun yi waiwaye kan wadansu daga cikin 'yan majalisar da suka rasu a baya-bayan nan: Sanata Mustapha Bukar, Sanata Ali Wakili, Hon Umar Buba, Hon Independence Ogunewe da kuma Hon Bello Sani.

An 'kashe barayin shanu 21' a Zamfara

Hukumomi a jihar Zamfara ta Najeriya sun ce za su yi aikin binne gawarwakin barayin shanu sama da 20 da sojoji suka hallaka a wata musayar wuta da suka yi da su tun daga ranar Talata har zuwa Alhamis.

Rundunar sojnin Najeriya ta ce an kashe mata sojoji biyu a arangamar da aka yi.

Bayanan hoto,

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatarwa da BBC wadannan bayanai

'Yan shara sun adabbi jihar Kaduna

Aikata muggan laifuka tsakanin al'umma na ci gaba da zama barazana a wadansu garuruwa na arewacin Najeriya, kamar jihar Kaduna, inda 'yan sara-suka ke cin karensu ba babbaka.

Baya ga matsalar da rikicin Boko Haram ya haddasa na rashin tsaro, wato sabuwar barazanar da ta sake dawowa bayan daukar lokaci da dainawa ita ce matsalar 'yan shara.

Za a bude gidan sinima na farko a Saudiyya

A karon farko cikin shekara 35 za a bude gidan sinima na farko a kasar Saudiyya a ranar 18 ga watan Afrilu.

Abin da zai share fagen bude wadansu gidajen sinimar kusan 100 a fadin kasar nan da shekarar 2030.

Bayanan hoto,

Matan Saudiyya na yawan kallon fina-finan kasashen Yamma - amma yawanci a sirri suke yin hakan

Za a rataye mutumin da ya saci giya a Najeriya

Wata kotu a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin satar kwalaban giya bakwai da kuma kwalin taba sigari daya.

A yayin yanke hukuncin da aka yi a ranar Laraba, alkalin babbar kotun ya samu mutumin da laifin fashi da kuma mallakar makamai da suka hada da adda da kuma gatari a yayin da ya je satar abubuwan.

An rantsar da sabon shugaban Saliyo a otel

An rantsar da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar adawa a kasar Saliyo, Julius Maada Bio a otal, bayan ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da ak agudanar.

Mista Maada Bio tsohon shugaban mulkin sojin kasar ne wanda ya yi mulki na wani dan takaitaccen lokaci a shekarar 1996.

Bidiyo: Yadda aka yi wa motar Man City ruwan kwalabe

Karanta karin wasu labaran

Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.