Najeriya: Sojoji sun 'kashe barayin shanu' sama da 20

Wuraren da sojoji suka fafata da barayin shanu
Bayanan hoto,

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatarwa da BBC wadannan bayanai

Hukumomi a jihar Zamfara ta Najeriya sun ce za su yi aikin binne gawarwakin barayin shanu sama da 20 da sojoji suka hallaka a wata musayar wuta da suka yi da su tun daga ranar Talata har zuwa Alhamis.

Rundunar sojnin Najeriya ta ce an kashe mata sojoji biyu a arangamar da aka yi.

Shugaban karamar hukumar Anka Moustapha Gado, ya ce sun soma shirye-shiryen zuwa wurin da lamarin ya faru da karin sojoji domin zakulo gawarwakin 'yan bindigar da aka kashe.

Ya ce daga nan za su binne barayin shanun a cikin babban rami domin kaucema barkewar cuttutuka.

Jihar ta Zamfara na fama da hare-haren da ake dora wa kan barayin shanu da 'yan fashi.

Ko a mkon jiya sai da aka kashe gwamman mutane a wani hari da aka kai wasu kauyuka.

Karanta karin wasu labaran

Yunkurin dakile hare-hare

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin makaman da aka kwace daga hannun masu satar shanu

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya Birgediya janarar Texas Chukwu, ya fada a cikin wata sanarwa cewa da dama daga cikin 'yan bindigar sun tsere tare da raunukan harbin bindiga.

Janarar Texas Chukwu ya ce sun kwato makamai da dama daga hannun 'yan bindigar, ciki har da bindiga samfurin AK47 da alburusai.

Sai dai babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatarwa da BBC wadannan bayanai.

A baya-bayan nan ne rundunar sojin sama ta kasar ta tura da dakaru na musamman zuwa Gusau, babban birnin jihar.

Ta ce an dauki wannan mataki ne domin dakile ayyukan barayin shanun da sauran masu aikata miyagun laifuka.

A kwanakin baya ne 'yan bindigar suka kaddamar da hare-hare a kauyukan karamar hukumar Anka lamarin da ya janyo mutuwar mutane da dama.