Salman Khan zai yi shekara 5 a gidan yari

Salman Khan
Bayanan hoto,

Salman Khan zai zauna a gidan yari na wani lokaci

Wata kotu a kasar India ta yankewa jarumin fina-finan Bollywood Salman Khan, hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar saboda ya yi farautar gwanki da ba kasafai ake samunta ba ba bisa ka'ida ba.

Kotun, wadda ke zamanta a Jodhpur, ta kuma ci tarar jarumin rupee 10,000 kwatankwacin dala 154.

Salman Khan dai ya kashe wasu nau'in gwanki da ake kira blackbucks guda biyu a yammacin jihar Rajasthan a yayin da ake daukar fim din Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

Kotun dai ta wanke sauran jaruman da suka fito a fim din tare su hudu.

Jarumin mai shekara 52, zai iya daukaka kara a kan hukuncin da kotun ta yanke masa.

Rahotanni sun ce dole ne Salman Khan ya zauna a gidan yari na wasu kwanaki.

Asalin shari'ar

Bayanan hoto,

Wannan ce tuhuma ta hudu da aka yi wa Salman Khan da ke da alaka da farauta a lokacin fim din

Wannan ne dai karo na hudu da ake shigar da karar jarumin a kan farautar dabbobi a lokacin da ake daukar fim dinsa na Hum Saath Saath Hain a shekarar 1998.

An wanke shi a kararraki ukun da aka shigar a baya.

A shekarar 2006, wata kotu ta tuhumi jarumin da laifuka biyu na farauta, inda aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara biyar.

To amma da shekara ta zagayo, wata babbar kotu a Rajasthan, sai ta yi watsi da hukuncin.

Ainahin shari'ar dai al'ummar yankin Bishnoi ne wadanda suke bauta wa dabbar da ya yi farautar ne suka shigar da ita.

Gwamnatin kasar dai ta daukaka kara a kan wanke jarumin a kotun koli.

An dai tuhumi jarumin da wasu mutum bakwai da kisan dabbobin daji da suka hada da gwanki a arewacin jihar Rajasthan.

Ya matsayin Salman Khan ya ke a India?

Salman Khan, na daya daga cikin jaruman Bollywood da suka yi fice, da kuma farin jini a wajen jama'a, ba ma a kasar kadai ba, har ma da wasu kasashen duniya.

Jarumin ya fito a fina-finai fiye da 100.

An fi sanin jarumin da fina-finan soyayya da ma na fada.

Ya kuma samu lambobin yabo da dama.

Sama da mutum miliyan 36 ne suke binsa a shafinsa na Facebook, inda ya ke da mutum miliyan 32.5 a shafinsa na Twitter.

Tausayin da aka ce ya ke da shi ga jama'a musamman tsofaffi da marayu, ya kara masa farin jini musamman a wajen talakawa.