Za a rataye mutumin da ya saci kwalaban giya a Najeriya

Giya

Wata kotu a jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin Najeriya, ta yankewa wani mutum hukuncin kisa ta hanyar rataya, bisa laifin satar kwalaban giya bakwai da kuma kwalin taba sigari daya.

A yayin yanke hukuncin da aka yi a ranar Laraba, alkalin babbar kotun ya samu mutumin da laifin fashi da kuma mallakar makamai da suka hada da adda da kuma gatari a yayin da ya je satar abubuwan.

Mai gabatar da karar na rundunar 'yan sandan jihar ya ce, mutumin da aka yankewa hukunci wato Raji Babatunde, na daga cikin wadansu gungun barayi hudu da suka yi fashi a wasu gidaje da ke Ado Ekiti.

Bayan fashin da suka yi na satar kwalaban giyar da kwalin tabar, mutumin da sauran abokan fashin nasa sun yi wa wani mutum fashin wayoyin salula kirar Nokia da kuma Techno.

Karanta wadansu labaran

'Yan sanda da ke aikin sintiri a ranar da lamarin ya afku sun ce, sun isa wajen da aka aikata fashin, inda suka kama Babatunde a daidai lokacin da yake kokarin guduwa, yayin da sauran mutum ukun kuma suka tsere.

Batun wannan hukunci da aka yankewa mutumin, ya janyo ce-ce-ku-ce a tsakanin wasu 'yan Najeriya.

Wasu na ganin cewa zai yi kyau da gwamnati za ta nemi a yanke hukunci irin wannan ga manyan mutane ciki har da 'yan siyasa wadanda ake zargi da wawure miliyoyin daloli daga baitul malin kasa.