Kalli hotunan 'yan Arsenal da suka kara da CSK Moscow

Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Lashe gasar ita kadai ce damar Arsenal ta zuwa gasar cin kofin Zakarun Turai badi

Alexandre Lacazette, Mesut Ozil da Hector Bellerin na cikin 'yan wasan Arsenal da suka yi atisayen karshe a ranar Alhamis kafin karawar da za su yi da CSK Moscow a wasan dab da na kusa da na karshe a gasar Europa.

Kusan duk 'yan wasan na nan lafiya kalau ban da Cazorla (wanda ke fama da rauni) sai Aubameyang (wanda ba zai buga ba).

Kalli hotuna 'yan wasan da Arsenal ta yi amfani da su a wasan:

'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Arsenal ta doke AC Milan a zagayen da ya gabata
'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Arsene Wenger ya ce kusan duk 'yan wasansa na cikin shiri domin tunkarar wasan
'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Aubameyang ba zai buga ba saboda ya wakilici Dortmund a baya a gasar
'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Jack Wilshare na taka rawar gani a 'yan kwanakin nan
'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Rashin Aubameyang zai kara bai wa Welbeck damar samun gurbi
'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Wasu na ganin Arsenal za ta iya lashe gasar ta bana
'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Sai dai babu tabbas ganin yadda suka sha da kyar a wasu wasannunsu na baya
'Yan wasan Arsenal Hakkin mallakar hoto Arsenal.com
Image caption Arsenal na fatan magoya bayanta za su cika filin wasa na Emirates ba kamar yadda wasu suka kaurace wa wasansu na ranar Asabar ba

Hotuna daga shafin intanet na Arsenal - ARSENAL.COM

Labarai masu alaka