Najeriya: Tallafin mai ya kai Naira tiriliyan 1.4

Dr Emmanuel Ibe Kachikwu

Asalin hoton, TWITTER

Bayanan hoto,

Dakta Emmanuel Ibe Kachikwu ya ce kamata ya yi a ce Najeriya tana ajiyar wannan kudi domin amfanin gaba

Karamin ministan albarkatun mai na Najeriya Dakta Ibe Kachikwu ya ce yawan kudin tallafin man fetur da gwamnati ke bayarwa a yanzu ya kai Naira tiriliyan 1.4.

Ministan ya bayyana hakan ne a wani taron karawa juna sani a Abuja ranar Alhamis, kan harkokin gas na girki (LPG), wanda gwamnati ke kokarin mayar da hankali a kansa domin rage matsi a kan fetur.

Dakta Kachikwu wanda ya jaddada bukatar ganin gwamnati ta adana wannan kudi ya ce kasar na bukatar kauce wa yawan dogaro ga fetur tare da bayar da fifiko a kan makamashi maras gurbata muhalli.

Dakta Kachikwu ya ce gwamnatin tarayya a cikin 'yan watanni masu zuwa za ta fito da wani tsari da zai magance matsalar karancin kayayyaki a bangaren mai da iskar gas.

Ya ce akwai bukatar bijiro da wasu manufofi da tsare-tsare da za su magance tarin kalubalen da ake fama da su a bangaren gas na girki ta yadda za a rika amfani da shi sosai a kasuwar cikin gida.