Tsohon shugaban Afrika ta Kudu Jacob Zuma ya gurfana a kotu

Asalin hoton, Reuters
A watan Fabrairu ne aka tilasta wa Jacob Zuma ajiye mukaminsa.
Tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu, Jacob Zuma ya gurfana a yau Juma'a a gaban babbar kotun Durban, bisa zargin cin hanci da rashawa dangane da wani ciniki na makamai tun a shekarun 1990.
Abu ne kamar mafarki, wai duniya juyi-juyi, domin kuwa mako takwas baya Jacob Zuma shugaban kasa ne, wanda kuma a wurin mutane da dama, gagararre ne, ba mai iya ce masa ko yi masa komai.
To amma jiya ba yau ba, domin kuwa a safiyar nan zai gurfana a matsayin karabitin dan kasa, a gaban alkali a babbar kotun birnin Durban.
Ana ganin wannan wani gagarumin cigaba ne ga matashiyar dumokuradiyyar Afirka ta Kudu.
Mista Zuma yana fuskar tuhuma 16 ne ta rashawa da zamba da almundahana da juya kudaden haram, sai dai ya musanta aikata wani abu na ba daidai ba.
Can baya a shekarar 2009 an yi watsi da tuhumce-tuhumcen a wani yanayi mai cike da sarkakiya.
Amma kuma sai suka sake tasowa yayin da ikonsa a kan jam'iyyarsa mai mulki ta ANC ya yi rauni.
Ga alama wannan shari'a za ta dauki dogon lokaci ana yinta, yayin da wata takaddamar ke neman kunno kai, kan ko gwamnati ce za ta ci gaba da biyan kudin dawainiyar shari'ar Mista Zuman.
Koma dai ya lamarin ya kasance, Juma'ar ta kasance wata rana ta daban, kasancewar ga tsohon shugaba Zuma gurfane a gaban shari'a, kuma abin da yawancin mutane ke dauka zamani na yi wa doka karan-tsaye sannan ruwa ta sha, ya zo karshe.
Duk da haka kuma wadanda suka rage cikin magoya bayan Mista Zuma da kuma iyalansa na bayyana shari'ar da bi-ta-da-kullin siyasa.
Suna masu cewa ana masa tuhumar ne kawai saboda ya mara baya ga tsauraran sauye-sauye na tattalin arziki.
To amma kuma hatta ita kanta jam'iyyarsa ta African National Congress, ANC, ta juya baya ga Mista Zuma, kuma daman bangaren shari'a na Afirka ta Kudun ya yi fice a batun 'yancin cin gashin-kai.