An daure tsohuwar shugabar Korea ta Kudu shekara 24

In this file photo taken on 23 May 2017 South Korean ousted leader Park Geun-hye arrives at a court in Seoul.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

A watan Mayun 2017 aka soma gurfanar da Ms Park a gaban kotun bayan an kama ta

Wata kotu a Koriya ta Kudu ta yanke hukuncin daurin shekara 24 kan tsohuwar shugabar kasar Park Geun-hye bayan an same ta da amfani da mukaminta ba bisa ka'ida ba da kuma yin karfa-karfa.

An watsa zaman kotun kai-tsaye inda aka yanke hukunci kan daya daga cikin manyan batutuwan da suka shafi aikata cin hanci a kasar, lamarin da ya kara rura wutar kyamar 'yan siyasa da attajirai.

Park, wacce aka ci tarar dala miliyan 17, ta yi fama da zarge-zargen cin hanci.

Tsohuwar shugabar ba ta halarci zaman kotun ba lokacin da aka yanke hukuncin.

Ta kauracewa sauraren shari'ar da ake yi mata a baya inda ta zargi kotunan kasar da yi mata bi-ta-da-kulli. Kazalika ta musanta aikata ba daidai ba sannan ta ce za ta daukaka kara.

Alkali Kim Se-yoon ya ce Park ba ta nuna wata alama "ta yin nadama ba" bayan ta sanya kasar cikin mawuyacin hali.

"Babu yadda muka iya illa mu dauki wannan mataki mai tsauri," in ji alkalin.

Ba a taba nuna yanke irin wannan hukunci kai tsaye a talabijin ba, sai dai hukumomi sun ce sun yi hakan ne saboda 'yan kasar na bukatar hakan.

South Koreans watch as the verdict is broadcast live

Asalin hoton, AFP/Getty

Bayanan hoto,

'Yan kasar Koriya ta Kudu sun kalli yanke hukuncin kai tsaye a talabijin

An samu Park da laifi 16 cikin 18 da aka zarge ta da aikatawa, wadanda akasarinsu na da alaka da batun cin hanci da kuma tilastawa mutane ba da rashawa.

Kotun ta ce tsohuwar shugabar kasar ta hada baki da babbar kawarta, Choi Soon-sil, inda suka matsa lamba kan kamfanoni irinsu Samsung domin su bayar da miliyoyin dala ga gidauniyar da Choi ke shugabanta.

An kuma same ta da laifin tursasawa kamfanoni domin su sanya hannu kan yarjejeniyar yin kasuwacin da kamfanonin Choi kana su bayar da kyautuka ga Choi da 'yarta.

Kazalika, an samu Park da laifin mika wasu takardun sirrin gwmanati da na ofishin shugaban kasa ga Choi.

Choi Soon-sil, the woman at the centre of the South Korean political scandal and long-time friend of President Park Geun-hye, arrives for a hearing arguments for South Korean President Park Geun-hye's impeachment trial at the Constitutional Court in Seoul, South Korea, 16 January 2017.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Choi (wacce ke tsakiya) tsohuwar kawar Park Geun-hye ce

Supporters of South Korea's former president Park Geun-hye gather during a rally demanding the release of Park Geun-hye outside the Seoul Central District Court in Seoul on 6 April 2018.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Magoya bayan Park sun taru a wajen kotun da ke Seoul inda suka bukaci a sake ta