Abubuwan da suka a Afirka na makon nan

A selection of the best photos from across Africa and of Africans elsewhere in the world this week.

Wani mutun na kwance lokacin da ake nuna gicewar itace na Yesu al -Masihu a ranar Good friday da aka yi a garin Lagos da ke Najeriya, wanda daga nan ake soma gudanar da shagulgulan Easter a ranar 30th ga watan Maris, 2018.. Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani mutun na kwance lokacin da ake nuna gicewar itace na Yesu al- Masihu a ranar Good friday da aka yi a garin Lagos da ke Najeriya.
Ana lallashin wata matashiya lokacin da ta ke kuka yayin nuna yadda aka giciye Yesu al-Masihu a lokacin bikin Easter da Good Friday a Lagos, Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana lallashin wata matashiya lokacin da ta ke kuka yayin nuna yadda aka giciye Yesu al-Masihu...
Masu ibada na yin adu'oi a ranar Easter a cocin Maria African Mission da ke unguwar marasa galihu ta Kibera a Nairobi da ke Kenya , a ranar 1 ga watan Afrilu,2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannna yaron yana adu'a cikin wani yanayi na nuna alhini a Nairobi babban birnin kasar Kenya
Harun Karanja, wanda shi ne ya malaki shagon Facebook Curio,na amfani da wayarsa domin ya duba shafinsa na Facebook a kusa da garin Mai Mahiu mai kwazazzabo da ke Kenya a watan Maris na shekarar 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harun Karanja, wanda shi ne ya malaki shagon Facebook Curio,na amfani da wayarsa domin ya duba shafinsa na Facebook a kusa da garin Mai Mahiu mai kwazazzabo da ke Kenya.
Maza na aiki a wurin gine-gine a Goma, babban birnin arewacin Kivu , da ke gabashin jamhuriyar Dimokradiyar Congo, a ranar 4 ga watan Afrilun, 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mutum na aiki a wurin gine-gine a Goma da ke gabashin jamhuriyar Dimokradiyar Congo .
Maza na aiki a wurin gine gine da ke Goma, babban birnin arewacin Kivu, a gabashin Jamhuriyar dimukradiyar Congo a ranar 4 ga watan Afrilu na 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ya yinda sauran suna aiki kan katakon da ake kafawa domin a yi gini .
Wani hoton marigayiya Winnie Madikizela Mandela da aka ajiye kan sanda mai dauke da tutar kasar Afrika ta kudu da jam'iyyar ANC a wani bango na tsohon gidan yari da ke Durban yayin da 'yan kasar suka taru domin tunawa da marigayiyar wadda ta rika fafitukar kawarda wariyar launin fata a taron adu'oin da aka yi da kyandira a garin Durban. a ranar 2 ga watan Afrilu 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A garin Durban na Afrika ta kudu, a ranar Litinin an sanya hoton Winnie Madikizela Mandela wadda ta rika fafitukar kawarda gwamnatin wariyar launin fata a taron adu'o'in da aka yi bayan rasuwarta tana da shekara 81 a duniya.
Mata wadanda mambobin jamiyyar ANC ne sun yi marci domin tunawa da mai fafitukar kawarda mulki wariyar launin fata da ta rasu Winnie Madikezela Mandela, tsohuwar matar shugaban kasan Afrika ta Kudu Nelson Mandela a Soweto , da ke garin Johannesburg a ranar 4 ga watan Afrilu na shekarar 20118 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Su kuma wadanan matan sun rika rera waka ne domin tunawa da ita a Soweto , inda Mrs Madikizela Mandela ta zauna wanda shi ne cibiyar masu fafitukar kwarada mulkin wariyar launin fata.
Jamian tsaro masu faretin ban girma a taron bankin raya kasashen musluncin karo na 43 a Tunis babban birnin Tunisa a ranar 4 ga watan Afrilu . Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A tunis babban birnin Tunisia , jamian tsaro sun yi faretin 'ban girma a ranar Laraba a taron bankin raya kassahen musulunci karo na 43
Gasar wasanni motsa jiki na Common wealth da ake yi a Gold Coast 2018 - bikin bude wasannin motsa jiki - filin wasa na Carrara - Gold Coast, a Australia - 4 ga watan Afrilu , 2018 - Salome Nyirarukundo 'yar Rwanda tana rike da tutar kasarta a lokacin bikin bude gasar. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A Australia kuma a wanna rana ,Salome Nyirarukundo 'yar Rwanda ta rike tutar kasarta a bikin bude wasanin motsa jiki na Commonwealth.
Masu talata kayan kawa sun sayan tufafin da Mark Johnson ya tsara a makon sanya kayan kawa da aka yi birnin Accra na kasar Ghana a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2018. Makon na samun masu dinki da kuma tsara kayan kawa da suka yi fice a yammacin Afrika da kuma Afrika bakidaya wadanda suke hadu wa domin nuna kayayakinsu daga ranar 29 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Juma'a wata mai talata kayan kawa na sanye da tufafin da aka dinka kuma aka gabatar a makon sanya kayan kawa.
Wata mata ta kada kuriarta a cikin akwatin zabe a wata rumfar zabe da ke Freetown a ranar 31 ga watan Maris , a zaben shugaban kasar Saliyo zagaye na biyu. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar, wata mata ta kada kuri'a a zaben shugaban kasa na saliyo zagaye na biyu .
Jama'a sun rika farinciki game da nasarar da Julius Maada Bio ya yi a ranar 4 ga watan Afrilu 2018 a birnin Freetown na kasar Saliyo People celebrate the victory of Julius Maada Bio. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sanarwar da aka yi a ranar Laraba, inda aka bayyana 'dan takarar 'yan hammaya Julius Maada Bio a matsayin wanda ya yi nasara ya sa magoyan bayansa sun rika murna da farinciki a Freetown babban birnin kasar.

Pictures from AFP, Reuters, EPA and Getty Images.