'Yan bindiga sun sako amaryar da suka sace a Birnin Gwari

An sako amaryar da aka sace da 'yar uwarta a Birnin Gwari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An sako amaryar da aka sace a Birnin Gwari

'Yan uwan amaryar da aka sace a Birnin Gwari na jihar Kaduna da ke Najeriya sun ce mutanen da suka yi garkuwa da ita sun sako ta tare da kanwarta ranar Juma'a.

Mijin amaryar ya tabbatar wa BBC da cewa an sako matarsa Halima da kuma kanwarta Shafa'atu da misalin karfe takwas na safe kuma yanzu suna kan hanyarsu ta zuwa Wushihi da ke jihar Niger.

Sai dai Ango bai bayanna cewa ko an biya kudin fansa ba kafin aka sako amaryar tasa ba, amma rahotanni sun ce sai da dangin amaryar suka biya naira miliyan daya kafin masu garkuwa da mutane su sako ta da 'yar rakiyarta.

Rahotanni sun ce masu garkuwa da mutane sun kai amaryar da kuma 'yar uwarta wani wuri da ake kira Tsohon Mai Unguwa da ke Birnin Gwari inda suka ajiye ta.

Tun farko angon ya shaida wa BBC cewa sun je daurin aure ne a karamar hukumar Ingawa ta jihar Katsina daga karamar hukumar Wushishi.

"Mun isa yankin Birnin Gwari ne da maraice kuma a lokacin daya daga cikin direbobin motar da ke dauke da amaryar ya fada hannun masu garkuwa da mutanen."

Daga nan ne sai masu satar mutanen suka tisa keyar amaryar da sauran 'yan uwanta da ke mata rakiya, kamar yadda angon ya bayyana.

Latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron cikakkiyar hirar BBC da angon kan yadda aka sace matarsa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Muryar angon da aka sace wa amarya a Kaduna

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a wani wuri mai nisan kilomita 55 da garin Birnin Gwari.

Sai dai rahotannin sun ce uku daga cikin wadanda aka sace daga cikin 'yan rakiyar amaryar sun tsere kuma sun koma garin a ranar Alhamis.

An dai bayyana hanyar Funtua a matsayin mai hadari sosai saboda masu garkuwar da mutane na afkawa mutane a kowane lokaci saboda tana tsakiyar kan iyakar Birnin Gwari da jihar Katsina.

Masu garkuwa da mutane sun rika kai wa yankin Birnin Gwari hare hare a baya bayanan.

Sojoji 11 ne aka kashe lokacin da masu garkuwa da miutane suka kai musu hari a wurin gudanar da bincike.

Labarai masu alaka