Kalli hotunan tseren keken mata zalla na farko a Saudiyya

Tseren keke a Saudiya Hakkin mallakar hoto Instagram/@jeddah_woman
Image caption Masu tseren keke sun shirya tsaf don tseren keke ta mata ta farko a Saudi Arabia

An gudanar da tseren keken mata na farko a kasar Saudiyya, inda suka bai wa mutane da yawa mamaki a kasar ta masu ra'ayin mazan-jiya, musamman a shafukan sada zumunta.

Wannan na cikin sauye-sauyen da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman yake bullowa da su a kasar, wanda suka hada da bude gidajen kallo, da kade-kade da raye-raye.

Haka kuma an bai wa mata izinin tuka mota a karon farko a kasar.

Kalli wadansu daga cikin hotunan tseren keken na mata zalla:

Hakkin mallakar hoto Social Media
Image caption Sun kimtsa kuma sun shirya tsaf domin shiga tseren keken mata na farko a kasar Saudiyya
Hakkin mallakar hoto Al Arabiya
Image caption Mata a wurin tseren keke na mata na farko a kasar Saudiyya. An rinka yada hotunan tseren a shafukan sada zumunta
Hakkin mallakar hoto Instagram/@jeddah_women
Image caption Mai shirya tsere Nadima Abu Al-Enein bayan da aka kammala tseren
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ba ta shiga cikin tseren ba: Wannan matar na tuka kekenta a birnin Jeddah

Labarai masu alaka