Masana'antun arewacin Najeriya za su farfado idan an gama aikin

Shugaban kamfanin mai na Najeriya, NNPC, Dokta Maikanti Baru (daga dama) lokacin da yake rattaba hannu a kan kwangilar shimfida bututan gas

Asalin hoton, NNPC

Bayanan hoto,

Dokta Maikanti Baru (daga dama) ne ya rattaba hannu a kan yarjejeniyar a madadin NNPC

Kamfanin man fetur na kasa a Najeriya, NNPC, ya bayar da kwangilar shimfida biyu daga cikin wasu bututan isakar gas guda uku da wasu tashoshin gas wadanda za su lashe kusan dala miliyan uku, wato sama da naira biliyan daya.

"Wannan kwangila ta tsare-tsare ce da samar da kayan aiki da kuma shimfida bututan", a cewar wata sanarwa da kamfanin na NNPC ya fitar.

Ana sa ran idan an kammala shi, wannan aiki zai taimaka wajen samar da makamashin da masana'antu ke bukata don samun wutar lantarki, lamarin da zai taimaka wajen farfado da masana'antu, musamman a gabashi da arewacin Najeriya.

Daya daga cikin kwangilolin ta shimfida bututun gas mai tsawon kilomita 200 ce daga cikin fiye da kilomita 600 da za a shimfida daga garin Ajaokuta na Jihar Kogi zuwa Kaduna zuwa Kano wanda ake yiwa lakabi da AKK.

Wannan bangaren bututun zai tashi ne daga Ajaokuta zuwa Abuja.

Wasu kamfanonin Najeriya biyu, Oando da OilServe aka bai wa kwangilar.

Daya kwangilar kuma ta shimfida karin kilomita 221 ta bututun na AKK ce ita ma, wadda aka bai wa hadakar kamfanin China Petroleum Pipeline Bureau da kuma Brentex.

Shi kuma wannan bututun zai tashi ne daga Kaduna zuwa Kano.

Mafarin aikin

Nan ba da jimawa ba, a cewar NNPC, za a bayar da kwangilar kashi na uku na aikin shimfida bututan.

A watan Disambar bara ne dai Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince a yi aikin shimfida bututan, a bisa tsarin hadin gwiwa a tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Najeriya ce ta fi kowacce kasa fitar da danyan mai a Afirka

A karkashin wannan tsari dai kamfanonin ne za su saka kudinsu, su tsara, su shimfida, su kuma tafiyar da bututan na wani lokaci, kafin daga bisani su zama na gwamnati—wato build, operate, and transfer a Turance.

Daukacin aikin shimfida bututan na AKK dai wani bangare ne na aikin shimfida bututan iskar gas a karkashin Babban Tsarin Samar da Iskar Gas na Kasa, wato Gas Infrastructure Blueprint a Turance.

An kirkiri wannan shiri ne da nufin taimakawa wajen samar da masana'antu a arewaci da gabashin Najeriya.

A gaba daya dai bututan za su tashi ne daga tashar mai ta Qua Iboe da ke Jihar Bayelsa zuwa tashar gas ta Cawthorne da ke Jihar Rivers sannan su ratsa ta Obigbo a Jihar ta Rivers.

Daga nan kuma sai su tafi su nufi Umuahia, babban birnin Jihar Abia su wuce Inugu, kafin kuma su zarce zuwa Ajaokuta.

Daga Ajaokutan ne kuma za su tashi zuwa Abuja, da Kaduna, da Kano.