WHO ta cika shekara 70 da kafuwa

Ma'aikaciyar lafiya a bakin aiki
Bayanan hoto,

Cikin shekara 70, WHO ta gudanar da ayyukan da suka shafi kiwon lafiya a duk fadin duniya.

A yau ne hukumar lafiya ta duniya WHO, ke bikin cika shekara 70 da kafuwa, kuma tun daga wancan lokacin take gudanar da ayyukan da suka shafi kiwon lafiya a duk fadin duniya.

WHO ta yi kira ga kasashen duniya su sake daura damarar inganta bangaren lafiya ga al'ummar kasashensu cikin shekara biyar mai zuwa.

Hukumar wadda Majalisar Dinkin Duniya ce ta kafa ta, ta ce cikin shekara 70 da suka wuce damar tsawon rayuwa ta karu da shekara 25, sannan yara miliyan shida na mutuwa kafin su kai shekara biyar idan aka kwatanta da shekarar 1990.

Kana kuma an yi nasarar rage cututtuka masu yaduwa kamar kyanda, da farankama da sauransu.

Sai dai hukumar ta kara da bayyana cewa har yanzu manyan kalubalen da take fuskanta na nan, wadanda suka danganci karuwar cutukan da ba masu yaduwa ba ne tsakanin jama'a.

Cutuka irin su cutar sukari da ta daji da kuma cutukan zuciya wadanda su ne ke sanadin mutuwa kashi 70 cikin dari a yau.