'An kama 'yan fashin da suka kashe mutane a Kwara'

Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idirs

Asalin hoton, NPF

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari ya ce an aika da karin jami'an tsaro Offa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce 'yan sandan kasar sun kama wasu daga cikin 'yan fashin da suka kai hari a garin Offa na jihar Kwara.

Harin, wanda aka kai kan wasu bankuna ranar Alhamis, ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 15.

A wani sako da shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya yi jaje ga daukacin mutanen da lamarin ya shafa.

"Muna mika jajenmu ga iyalai da mazauna Offa, da kuma gwamnati da jama'a jihar Kwara, kan mummunan harin da 'yan fashi da makami suka kai kan bankuna.

"Jami'an 'yan sanda sun kama da dama daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a kai harin sannan an tura karin jami'an tsaro garin domin su taimaka wajen bincike da tabbatar da tsaro", in ji shugaban.

Harin da aka kai garin na Offa ya janyo mummunan alla-wadai daga 'yan kasar, musamman masu amfani da shafukan sada zumunta da muhawara.

Hasalima, an kirkiro da wani maudu'i mai suna offa a shafin Twitter domin yin tur da harin.

Najeriya dai na fama da matsalolin rashin tsaro, a daidai lokacin da masana ke ganin jami'an tsaron kasar ba su da yawan da za su kare jama'a.