An kama limamin cocin Katolika kan bidiyon batsa na yara

Vatican Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A 1993 Monsignor Capella ya zama limamin cocin na Katolika sannan ya zama jami'in diflomasiyyar fadar Cocin a 2004.

'Yan sandan fadar Paparoma wato Vatican sun kama wani limamin coci wanda ake zargi da saba dokokin hoton bidiyon batsa na yara.

Ana tsare da Monsignor Carlo Alberto Capella a daya daga cikin kurkuku na fadar shugaban darikar Katolikan na duniya.

Kafin ya shiga hannu limamin cocin yana aiki ne a ofishin jakadanci na fadar ta Vatican a babban birnin Amurka, Washington.

Tun a shekarar da ta wuce ne jami'an Amurka da na Canada suka fara gudanar da bincike a kan malamin bisa zargin mallakar hotunan bidiyo na batsa na yara, abin da ya sa fadar Paparoman ta dawo da shi a watan Satumba.

Daga nan ne ita ma ta fara gudanar da bincikenta abin da ya kai yanzu ga tsare shi.

Wakilin BBC a birnin Rum ya ce galibi ana sukar Cocin ta Katolika da kokarin kare limamanta amma a wannan karon fadar ta Paparoma ta dauki mataki da sauri.