Gobarar Trump Tower ta halaka mutum guda

Trump Tower
Bayanan hoto,

Gobarar ta tashi ne a hawa na 50 na dogon benen na Trump Tower

Mutum guda ya mutu kuma masu kashe gobara hudu sun sami raunuka bayan da dogon benen Trump Tower ya kama da wuta a birnin New York.

Masu kashe gobara sun ce mutumin wanda mazaunin benen ne ya mutu ne bayan an kai shi asibiti.

Shugaban Amurka Donald Trump na da gida da ofis a benen, amma matarsa Melania da dansu Barron na birnin Washington DC.

Gobarar ta tashi ne a hawa na 50 na benen wanda akasari ke dauke da ofisoshi da gidajen zama.

'Yan kwana-kwana a New York suna can suna kokarin kashe wata gobara da ta tashi a hawa na 50 na ginin Hasumiyar Trump, ta shugaban Amurka.

Babban jami'in kashe gobara na birnin ya ce mutum daya da gobarar ta ritsa da shi a wani daki a cikin katafarn dogon benen, yana cikin mawuyacin hali.

Haka kuma 'yan kwana-kwana hudu daga cikin masu aikin shawo kan gobarar sun ji raunuka, amma an ce ba masu hadari ba ne.

Babban jami'in kashe gobarar Daniel Nigro ya ce gobara ce mai wahalar kashewa, kuma hayaki mai yawa ya turnuke sauran sassan ginin, lamarin da ya kara tsanani ga aikin.

Bayanan hoto,

Masu kashe gobara da ma'aikatan agajin gaggawa da ke wurin sun kai 200

Akwai ma'aikatan kwana-kwana 200 tare da jami'an bayar da agajin gaggawa a wurin.

Ginin shi ne hedikwatar Kamfanin Trump, mallakin Shugaba Donald Trump na Amurka, wanda aka ce yana Washington a yanzu.

Shugaban ya aike da sakon godiya ta Tweeter ga ma'aikatan kashe gobarar, yana mai cewa gini ne hadadde da aka yi shi da kyau.