Gobarar Trump Tower ta halaka mutum guda

Fire trucks arrive outside Trump Tower on 5th Avenue in New York on April 7, 2018 Hakkin mallakar hoto AFP/Getty Images
Image caption 'Yan kwanan-kwana suna gaban ginin na Trump Tower da ke birnin New York

Mutum guda ya mutu kuma masu kashe gobara hudu sun sami raunuka bayan da dogon benen Trump Tower ya kama da wuta a birnin New York.

Masu kashe gobara sun ce mutumin wanda mazaunin benen ne ya mutu ne bayan an kai shi asibiti.

Shugaban Amurka Donald Trump na da gida da ofis a benen, amma matarsa Melania da dansu Barron na birnin Washington DC.

Gobarar ta tashi ne a hawa na 50 na benen wanda akasari ke dauke da ofisoshi da gidajen zama.

Kawo yanzu jami'ai ba su tabbatar da dalilin wannan gobarar ba.

Kwamishinan 'yan kwana-kwana na jihar New York, Daniel Nigro ya yi gargadin cewa "har yanzu da sauran hatsari saboda mtaukar yawan hayaki daga ginin".

Ya kara da cewa "Mun tarar da gobara a hawa na 50 na benen. Ma'aikatanmu sun yi namijin kokari inda suka kutsa cikin gidan da ya ke ci da wuta gaba dayansa."

"Mun sami mutum guda a ciki wanda a halin yanzu ke cikin mawuyacin hali."

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Akwai ofisoshi da gidajen zama a benen Trump Tower da ke birnin New York

Labarai masu alaka