Abubuwan da suka faru a Afirka a wannan makon

Wasu daga cikin hotuna mafi kyau na abubuwan da suka faru a Afirka da wadansu wuraren a makon nan.

Wani mutun na kwance lokacin da ake nuna giccewar itace na Yesu al -Masihu a ranar Good friday da aka yi a garin Lagos da ke Najeriya, wanda daga nan ake soma gudanar da shagulgulan Easter a ranar 30th ga watan Maris, 2018.. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mutun na kwance lokacin da ake nuna giccewar itace na Yesu al-Masihu a ranar Good friday da aka yi a garin Lagos da ke Najeriya.
Ana lallashin wata matashiya lokacin da ta ke kuka yayin nuna yadda aka gicciye Yesu al-Masihu a lokacin bikin Easter da Good Friday a Lagos, Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana lallashin wata matashiya lokacin da ta ke kuka yayin nuna yadda aka gicciye Yesu al-Masihu...
Masu ibada na yin addu'oi a ranar Easter a cocin Maria African Mission da ke unguwar marasa galihu ta Kibera a Nairobi da ke Kenya, a ranar 1 ga watan Afrilu, 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan yaron yana addu'a cikin wani yanayi na nuna alhini a Nairobi babban birnin kasar Kenya
Harun Karanja, wanda shi ne ya mallaki shagon Facebook Curio,na amfani da wayarsa domin ya duba shafinsa na Facebook a kusa da garin Mai Mahiu mai kwazazzabo da ke Kenya a watan Maris na shekarar 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Harun Karanja, wanda shi ne ya mallaki shagon Facebook Curio, na amfani da wayarsa domin ya duba shafinsa na Facebook a kusa da garin Mai Mahiu mai kwazazzabo da ke Kenya
Maza na aiki a wurin gine-gine a Goma, babban birnin arewacin Kivu, da ke gabashin jamhuriyar Dimokradiyar Kongo, a ranar 4 ga watan Afrilun, 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani mutum na aiki a wurin gine-gine a Goma da ke gabashin jamhuriyar Dimokradiyar Kongo.
Wasu maza ma'aikata a wurin gine-gine da ke Goma, babban birnin arewacin Kivu, a gabashin Jamhuriyar dimukradiyar Congo a ranar 4 ga watan Afrilu na 2018. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Yayin da sauran ma'aikata ke aiki kan katakon da ake kafawa domin a yi gini.
Wani hoton marigayiya Winnie Madikizela Mandela da aka ajiye kan sanda mai dauke da tutar Afrika ta kudu da jam'iyyar ANC a wani bango na tsohon gidan yari da ke Durban yayin da 'yan kasar suka taru domin tunawa da marigayiyar wadda ta rika fafitukar kawar da wariyar launin fata a taron addu'oin da aka yi da kyandira a garin Durban. a ranar 2 ga watan Afrilu 2018. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Litinin an sanya hoton Winnie Madikizela Mandela wadda ta rika fafitukar kawar da gwamnatin wariyar launin fata a taron adu'o'in da aka yi a garin Durban na Afrika ta kudu, bayan rasuwarta tana da shekara 81 a duniya.
Mata wadanda mambobin jamiyyar ANC ne sun yi maci domin tunawa da mai fafitukar kawarda mulki wariyar launin fata da ta rasu Winnie Madikezela Mandela, tsohuwar matar shugaban kasan Afrika ta Kudu Nelson Mandela a Soweto, da ke birnin Johannesburg a ranar 4 ga watan Afrilu na shekarar 20118 Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Su kuma wadannan matan sun rika rera waka ne domin tunawa da ita a Soweto, wurin da Mrs Madikizela Mandela ta zauna wanda shi ne cibiyar masu fafitukar kawar da mulkin wariyar launin fata.
Jami'an tsaro masu faretin ban girma a taron bankin raya kasashen musluncin karo na 43 a Tunis babban birnin Tunisiya a ranar 4 ga watan Afrilu. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A Tunis babban birnin Tunisiya, jami'an tsaro sun yi faretin 'ban girma a ranar Laraba a taron bankin raya kasashen Musulmi karo na 43
Gasar wasannin motsa jiki na Commonwealth da ake yi a Gold Coast 2018 - bikin bude wasannin motsa jiki - filin wasa na Carrara - Gold Coast, a Ostreliya - 4 ga watan Afrilu , 2018 - Salome Nyirarukundo 'yar Rwanda tana rike da tutar kasarta a lokacin bikin bude gasar. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A Ostreliya kuma a wannan ranar, Salome Nyirarukundo 'yar kasar Rwanda ta rike tutar kasarta a bikin bude wasanin motsa jiki na Commonwealth.
Masu tallata kayan kawa sun sayan tufafin da Mark Johnson ya tsara a makon sanya kayan kawa da aka yi birnin Accra na kasar Ghana a ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2018. Makon na samun masu dinki da kuma tsara kayan kawa da suka yi fice a yammacin Afrika da kuma Afrika bakidaya wadanda suke haduwa domin nuna kayayakinsu daga ranar 29 ga watan Maris zuwa ranar 1 ga watan Afrilu. Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption A ranar Juma'a wata mai tallata kayan kawa na sanye da tufafin da aka dinka kuma aka gabatar a makon sanya kayan kawa.
Wata mata ta kada kuri'arta a cikin akwatin zabe a wata rumfar zabe da ke Freetown a ranar 31 ga watan Maris, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Saliyo. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A ranar Asabar, wata mata ta kada kuri'a a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar Saliyo.
Jama'a sun rika farin ciki game da nasarar da Julius Maada Bio ya yi a ranar 4 ga watan Afrilu 2018 a birnin Freetown na kasar Saliyo. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sanarwar da aka yi a ranar Laraba, inda aka bayyana 'dan takarar 'yan hamayya Julius Maada Bio a matsayin wanda ya yi nasara ya sa magoyan bayansa sun rika murna da farin ciki a Freetown babban birnin kasar.

Hotuna AFP, Reuters, EPA da kuma Getty Images.