Kalli yadda gobara ta kama benen Shugaba Trump

Gobara ta tashi a Trump Tower a New York, kuma masu kashe gobara hudu sun sami raunuka, inda akalla mutumm guda ya mutu.

Wannan hoton na nuna lokacin da gobarar ke ci gadan-gadan a hawa na 50 na bene Trump Tower a ranar Asabar,

Asalin hoton, Reuters/@ZionLee

Bayanan hoto,

Wannan hoton na nuna lokacin da gobarar ke ci gadan-gadan a hawa na 50 na bene Trump Tower a ranar Asabar

Asalin hoton, AFP/Getty Images

Bayanan hoto,

Motocin kashe gobara sun isa benen Trump Tower domin kashe gobara a titin Fifth Avenue da ke birnin New York

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Hayaki ya turnuke benen Trump Tower har ma da benaye da ke kusa a yayin da gobara ke tashi a benen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wannan hoton na nuna yadda tagogin bene Trump Tower suka fashe bayan gobarar da ta kama a hawa na 50 na benen

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

A nan ma wasu motocin kashe gobara ne suka isa benen Trump Tower a titin Fifth Avenue da ke birnin New York domin kashe gobarar

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Ana iya ganin yadda gobara ta shafi ginin, kuma akwai gidajen zama da ofisoshi a benen Trump Tower da ke birnin New York

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Wata motar kashe gobara na barin bene Trump Tower bayan an sami kashe gobara a birnin New York

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan kwana-kwana na birnin New York na barin ginin bayan da suka kashe gaobarar a birnin New York