Burtaniya: An nada zakaran Gasar Miji Ya Goya Matarsa na bana

A man carrying his 'wife'
Bayanan hoto,

Chris Hepworth da matarsa Tanisha a lokacin gasar ta bana

Ma'aurata daga sassa daban-daban na duniya sun jure tabo da ruwa da kududdufai a Gasar Miji Ya Goya Matarsa ta Birtaniya.

Maigida Chris Hepworth wanda ke goye da matarsa Tanisha Prince ne suka lashe gasar ta bana bayan da suka yi nasarar kammala tseren mai nisan mita 380 a Surrey na kasar Ingila.

Masu shirya gasar sun ce an fara ta ne a watan Yunin shekarar 793 Miladiyya.

Wadanda suka shiga gasar na fuskantar wani hawa mai tsawon kafa 49 da sauka a cikin tseren, wanda masu shiryawa suka bayyana shi a matsayin "mai wahalswa".

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Tseren fanfalaki ne na mita 380 ne da ya hada da hawa da gangara

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Chris Hepworth da matarsa Tanisha ne zakarun gasar ta bana

A karkashin dokokin gasar, dole dukkan matan da za a goya su kasance sun kai shekaru 18 da haihuwa - kuma kada su kasa kilogram 50.

Yar da matar da ake goye da ita laifi ne wanda zai sa a rage wa masu laifi maki.

Zakaran gasar, Mista Hepsworth ya ce yayi "mamakin nasarar da suka samu", ya kuma yaba wa matarsa, inda ya ce hawa ya fi wahalar da shi ba sauka ba.

Wannan nasarar ta ba su damar shiga Gasar Miji Ya Goya Matarsa ta duniya da za a yi a kasar Finlan a watan Yuli.

"Wa ya sani ko mune za mu lashe wannan gasar ta duniya ma", inji Mista Hepworth.

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Gasar ta yi armashi inda fiye da ma'aurata 50 ne suka shiga gasar ta bana

Masu shirya gasar sun gargadi wadanda suka shiga gasar cewa: "Gasar Goyon Mata na da hatsari, kuma yana iya janyo raunuka kamar gocewar kashin baya, da karaya a kafa da hannuwa, da daujewa a fuska da hujewar kashin kai da kuma sauran raunuka da rashin lafiya, wadanda suka hada da mutuwa."

Amma sun ce, "Kada ku bari wannan gargadin ya tsorataku!"

Wasu ma'aurata - Ben da Hannah Brackenbury sun shiga gasar ne domin bikin ranar aurensu na shekara guda. Tun daga Amurka suka je wajen wannan gasar ta bana.

Ma'auratan sun dauki lokaci suna shirya wa wannan gasar a filin da ke bayan gidansu, cikin ruwan sama.

Bayanan hoto,

Ben da Hannah Brackenbury sun shiga gasar ne domin bikin ranar aurensu na shekara guda

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

An yarda da goyo iri daban-daban a gasar

Zakarun gasar sun karbi kyautar wata gangar giya da ake hada ta a garin, inda wadanda suka yi na karshe suka karbi taliya da abincin kare.

Bayanan hoto,

Zakarun gasar bana na shirin zuwa Gasar Goyon Mata na duniya a Finland

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Wasu 'yan wasan goyon mata na tsallake tarin ciyawar da aka saka a hanyar domin kara wa gasar armashi