Najeriya: Buhari zai fara ziyarar aiki a Burtaniya

Shugaba Buhari

Asalin hoton, Getty Images

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai fara wata ziyarar aiki a Burtaniya, inda ake sa ran zai gana da firayi ministar kasar Theresa May da shugannnin wasu kamfanonin hakar mai.

Ana sa ran shugaban ya bar Abuja zuwa birnin Landan a ranar Litinin.

Bayan ganawa da Misis Theresa May, ana sa ran shugaban zai halarci taron shugabannin kasashen kungiyar rainon Ingila - Commonwealth daga 18 ga watan Afrilu 2018.

Shugaba Buhari zai kuma gana da shugaban kamfanin mai na Royal Dutch Plc, Mista Ben van Beurden, da na kamfanin mai na Shell, dangane da batun zuba jari na dala biliyan 15 a tattalin arzikin Najeriya.

Bayanan na cikin wata sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu, ya raba wa kafofin watsa labarai.

Sanarwar ta ce shugaban na Najeriya na kallon ganawar a matsayin wata damar tallafa wa tattalin arzikin Najeriya na shekara 20 masu zuwa.

Sanarwar ta kuma ce shugaba Buhari zai tattauna da Archbishop na Canterbury Justin Welby, wanda abokinsa ne, domin inganta zamantakewa tsakanin mabiya addinai daban-daban na cikin kasar da ma duniya.

Shugaba Buhari zai kuma gana da wasu manyan jami'ai daga Burtaniya da 'yan Najeriya masu zama a kasar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Shugaba Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo yayin da ya dawo Najeriya daga Landan a bara