Nigeria: An kashe Mutum 1,300 a jihar Zamfara

Wasu sarakuna a Zamfara sun ce za su nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya don kawo karshe matsalar tsaro a jihar.

Asalin hoton, ZAMFARA GOVERNMENT

Bayanan hoto,

Wasu sarakuna a Zamfara sun ce za su nemi taimakon Majalisar Dinkin Duniya don kawo karshe matsalar tsaro a jihar.

Gwamnatin jihar Zamfara ta ce akalla mutane 1,320 ne aka tabbatar sun mutu a shekaru bakwai da barayin shanu suka kwashe suna kai hare-hare kan kauyukan jihar.

Haka kuma gwamnatin jihar ta ce an raunata wasu mutane kusan dubu biyu kuma an lalata gidaje da gonaki fiye da dubu goma.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta tura runduna sojojin sama zuwa jihar domin taimakawa wajen fatattakar barayin.

A wata hira da BBC, sakataren Gwamnatin Jihar Farfesa Abdullahi Muhammad Shinkafi ya ce a halin yanzu gwamnatin jihar tana bayar da tallafin kudade da sauran kayayyaki ga wadanda lamarin ya rutsa dasu.

Gwamnatin jihar Zamfara dai ta ce matsalar rikicin masu satar shanu da ke ci gaba da janyo asarar rayuka da dukiyoyi ba za ta rasa nasaba da hannun wasu ba da ba sa son jihar ta zauna lafiya.

Cikin watannin da suka gabata barayin shanu sun yi ta kai hare-haren da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da jikkata wasu.