An kai hari da makamai masu linzami a Syria

Yakin da ake tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin Syria, ya lalata garin Ghouta Hakkin mallakar hoto AF/GETTY IMAGES
Image caption Yakin da ake tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin Syria, ya lalata garin Ghouta

Kafar sadarwar Syria ta ce an kai hari da makamai masu linzami a wani filin tashin jiragen saman sojin kasar a wajen garin homs.

Kafar ta ce mutune da dama ne su ka mutu a filin jirgin da Isra'ila ta yi kokarin kai wa hari a watan Fabrairu a wani yunkuri na ramuwar gayya.

Syria ta zargi Amurka da kai harin wanda ya faru sa'o'i bayan da Shugaba Trump ya ce Bashar Al-Assad zai dandana kudarsa bisa zarginsa da ake yi na kai hari da makamai masu guba a kusa da Damascus.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta musanta zargin.

A ranar Litini kuma ake saran Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya zai gudanar da taro domin tattauna zargin amfani da makami mai guba a Syriar.

Kuma gabannin kiran wannan taro kasashen duniya sun ci gaba da yin Allah wadai da harin, musanman bayan an yita yada hotunan mata da kananan yara da suka mutu a harin, ko da yake kawo yanzu ba a iya tantance gaskiyar hotunan ba.

A martani daya mayar shugaban Amurka Donald Trump ya zargin shugaba Putin na Rasha da kuma kasar Iran kan amfani da gubar a harin na ranar asabar -inda ya bayyana shugaba Assad na Syria a matsayin dabba.

Shugaba Trump ya ce tabbas wadanda suka aikata wannan dayen aiki za su girbe abun da suka shuka.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta gargadi Amurka da kada ta ce zata yi amfani da karfin soji saboda abun daya kira kazafi da aka kitsa, tana mai cewa matukar Amurka ta dauki matakan soji akwai mummunar sakamako.

Anata bangaren gwamnatin Syria ta fitar da sanarwa a hukumance tana mai cewa a duk lokacin da dakarun gwamnati suka kara matsawa yankuna da 'yan tawaye suka mamaye, wasu ke zargin amfani da makami mai guba.

A bangare guda kuma rahotanni sun ce an shiga zagayen karshe na mika wuya da 'yan tawaye ke yi a wasu yankunan da aka yiwa kawanya, inda kashin farko na 'yan twayen da iyalan su suka fice daga garin Douma.

Hakan ya biyo bayan makwanni da aka kwashe ana bata ta kashi inda yankunan da 'yan tawaye ke iko suka yi ta fama da hare haren ta hare, da kuma harin da ake zargin sojojin Syria da amfani da makami mai guba:

Labarai masu alaka