Shugaba Buhari zai tsaya takara a 2019

buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya sanar da cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.

Mai taimakawa shugaban na musamman kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Wannan sanarwa dai ta zo ne bayan da aka shafe swatanni ana yada jita-jitar ko zai tsaya ko ba zai tsaya ba takarar ba.

Sai dai tun kafin shugaban ya bayyana aniyar tasa akwai wadanda suke ganin bai kamata ya nemi tazarce ba, ciki har da tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo.

'Buhari ba zai so ya bar gwamnati yanzu ba'

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/BUHARI SALLAU

Jama'a da dama na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan sanarwar da Shugaba Buhari ya yi cewa zai nemi tazarce a zabe mai zuwa.

Sai dai Dr Suleiman Amu Suleiman, masanin siyasa a Jami'ar East Anglia da ke Birtaniya, ya shaida wa BBC cewa bai yi mamakin sanarwar ba.

Ya ce hauhawar da farashin mai da ake yi a baya-bayan nan, ya nuna cewa kudi zai ci gaba da shigowa gwamnati domin samun damar yin ayyuka da cika alkawuran da ya dauka sakamakon lokacin da ya samu gwamnatin cikin talauci.

Don haka babu wanda zai so ya bar gwamnati a yanzu.

Abu na biyu shi ne, shugaban ya samu lafiya sosai fiye da shekarar da ta gabata, lokacin da hankalin wasu da dama ya tashi saboda tabarbarewar lafiyarsa.

A yanzu ya samu kwarin gwiwa yana tafiye-tafiye ba tare da wata matsala ba.

Abu na uku shi ne, ' Ina ganin shi kansa Shugaba Buhari yana ji a zuciyarsa cewa bai taka rawar azo-agani ba, a don haka yana so a sake bashi dama domin ya gyara'.

Nasarar da ya samu ba ta kai wacce ya samu ba a lokacin da ya shugabanci Hukumar Kula da Kudaden da ake samu na rarar man fetur inji Dr Suleiman.

Idan har ya wuce to zai samu damar yin ayyuka ba tare da wani dabaibayi na siyasa ba irin wanda ya makale shi a shekara hudunsa na farko.

Sai dai ' Ba zan iya cewa zai kai labari ba tukunna domin wannan zai dogara ne kan irin shirin da 'yan adawa suka yi, da yadda ra'ayin 'yan Najeriya zai karkata kafin lokacin'.

Dama dai tun kafin wannan sanarwa wasu masu sharhi su ka fara tofa albarkacin bakinsu kan yiwuwar sake tsayawar Buharin takara.

Malam Jafar Jafar wani mai sharhi ne kan harkokin siyasar Najeriya, kuma ya ce yana ganin duk wani dan siyasa da yake neman takara a jam'iyyar APC yana bata wa kansa lokaci ne kawai, "matukar Shugaba Buhari zai sake yin takara."

Ya ce: "Idan har Buhari zai yi takara, to babu makawa jam'iyyarsa shi za ta tsayar a zaben 2019."

"Kuma da wahala a ce ba zai yi takara ba," in ji shi.

Malam Jafar ya ce zabin da ya rage masu muradin yin takara a jam'iyyar APC shi ne kawai su sauya jam'iyya.

"Ga jam'iyyu nan da yawa. Idan dai ba a yi murdiya ba a zaben 2019, akwai yiwuwar jam'iyyar APC za ta iya faduwa zabe."

"Saboda a gaskiya farin jinin jam'iyyar da na Shugaba Buhari ya ragu sosai."

Zuwa yanzu dai Shugaba Buharin da kuma gwamnan jihar Ekiti da ke kudu maso yammacin kasar Ayo Fayose ne kawai suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugabancin kasar.

 • Shugaba Buhari ya ci zabe ne a shekarar 2015
 • Ya yi takara sau hudu a jere kafin ya samu nasara
 • Shi ne dan takara daga jam'iyyar adawa na farko da ya doke shugaba mai ci a tarihin Najeriya
 • Ya samu kuri'u 15,424,921
 • Ya yi ta fama da jinya a shekarar 2016 inda ya shafe fiye da wata uku a Birtaniya

Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

Hakkin mallakar hoto Photoshot
Image caption Wata mai goyon bayan Buhari na sumbatar hotonsa da aka manna
 • Shekararsa 72
 • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
 • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
 • An hambare shi a juyin mulki
 • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
 • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
 • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
 • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
 • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa

Labarai masu alaka