Ba ra'ayin Buhari ba ne sake tsayawa takara - Sha'aban Sharada

Bayanan sauti

Hirar Sha'aban Sharada kan sake tsayawar Buhari takara

Latsa alamar lasifikar da ke sama don jin cikakkun kalaman Sha'aban Sharada:

Jim kadan bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana aniyyarsa ta sake tsayawa takara a 2019, kasar ta dauki dumi, inda jama'a ke ta tofa albarkacin bakinsu.

Wani mai taimakawa shugaba Buharin kan harkokin watsa labarai Sha'aban Sharada, ya shaida wa BBC cewa Shugaba Buharin bai ayyana aniyarsa ta sake tsayawa takarar bisa ra'ayin kansa ba sai don ra'ayin al'ummar kasa.

Ya ce: "Da a son ran Shugaba Buhari ne da ba zai sake tsayawa takarar neman shugabancin Najeriya ba. Komawa Kaduna ko Daura zai yi ya zauna ya huta ya yi ta shan fura yana salati, domin babu abun da yake bukata a duniya."

Wasu masu sharhi a kasar dai na ganin na kusa da Shugaba Buharin ne suka matsa masa lamba don sake tsayawa takarar saboda su na so a ci gaba da damawa da su a gwamnati.

Amma Malam Sha'aban ya ce: "Babu mamaki idan na kusa da shi sun matsa masa ya fito, amma sai dai za su yi hakan ne don sun ga irin jerin ayyukan da yake so ya yi a kasar wadanda 'yan Najeriya ba za su gani a kasa ba sai nan da shekara biyu zuwa uku."

To don jin cikakkiyar hirar da Naziru Mika'ilu ya yi da Sha'ban Sharada sai a latsa alamar lasifikir da ke sama don sauraro: