Najeria: Sojoji sun kubatar da mutum 149 daga hannun BH

Sojojin sun kubatar da mata 54 da kuma yara 95
Image caption Sojojin sun kubatar da mata 54 da kuma yara 95

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kubatar da mutum 149 daga hannun mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sojojin sun kashe mayaka Boko Haram uku ya yin da suka kama biyar a farmakin da sojojin suka kai a karshen mako.

Rundunar sojojin Najeriya ta ce sanar cewa ta kubatar da mutane da dama da 'yan Boko Haram suke garkuwa da su a watannin da suka gabata .

A cikin wadanda aka a ceto a baya-bayan nan akwai mata 54 da kuma yara 95.

Kakakin rundunar sojin kasa ta Najeriya kanal Onyeama Nwhachukwu, a cikin wata sanarwa ya ce sojojin aikin kakkabe sauran mayakan BH da suka rage a dajin Sambisa lokacin da suka gano mutanen da ake garkuwa da su.

A wani labarin kuma 'yan kurnar bakin wake biyu ne suka hallaka lokacin da suka yi kokarin cikin garin Konduga a ranar Asabar


Boko Haram a takaice

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abubakar Shekau shi ne shugaban Boko Haram tun 2009
  • An kafa ta a shekarar 2002
  • Sunanta da Larabci shi ne, Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati wal-Jihad
  • Ta fara aikinta ne da nuna kin jinin karatun boko
  • Ta kaddamar da kai hare-hare a shekarar 2009 da zummar samar da daular musulunci
  • Amurka ta ayyana ta a matsayin kungiyar ta'adda a 2013
  • Kungiyar ta ayyana wasu yankuna da ta kame a matsayin daulolin musulunci a shekarar 2014
  • A yanzu haka sojoji sun kwato mafi yawan yankunan

Labarai masu alaka