Sakin mata ya zama kamar shan ruwa – Sarki Sunusi

Sarkin Kano ya ce yada ake yawan sakin mata a cikin alumma a ya koma tamkar kamar ruwan sha Hakkin mallakar hoto dailytrust
Image caption Sarkin Kano ya ce yadda ake yawan sakin mata a cikin al'umma ya koma tamkar kamar ruwan sha

An bude wani taro kan hakkin mata a gidajen aure da kuma sha'anin gado a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar.

Taron wanda ofishin ministan kula da farfado da martabar al'adu tare da hadin gwiwar mai martaba Sarkin Kano suka shirya, zai kuma yi magana a kan shugabancin na gari.

A jawabin da ya yi, mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, ya yi wa hukumomin Nijar tuni a kan nauyin da ya rayata kan shugabanni a musulunce.

"Mu da muke ganin muna zaune da matanmu da 'ya'yanmu suna karatu yanzu muna fitowa mutane suna cewa Allah ya kara maka imani, lokacin da 'ya'yanmu suka zo matsayimu suka fito, jifan su za a rika yi",

"Saboda haka duk wani mutumin da Allah ya dorawa shugabanci na al'umma a wannan a lokaci, Allah ya dora masa nauyin da zai dauki matakai don ya gyara wannan gaba, saboda 'ya'yanmu da jikokinmu da ke biyo baya", a cewar mai martaba Sarkin Kano.

Daga bisani mai martaba sarkin Kano ya nuna damuwa kan yadda ake yawan sakin matan aure.

"Abin da ya fi ban tsoro shi ne yadda ake sakin mata da 'ya'ya, saki a cikin al'ummarmu ya zaman kamar shan ruwa.

"Duk sanda ka damu, wani abu ya dame ka, sai ka ce na sake ki koma gidan iyayenki, da ita da 'ya'yan da ta haifa maka ka mayar wajen mahaifinta, ba ka san cinta ba, ba ka san shanta ba, ba ka san kula da 'yayanka ba".

"Idan mahaifin ba shi da hali, shi kenan 'ya'yanka sun shiga duniya sai abin da da suka zama," in ji Sarki Muhammadu Sanusi.

Shugaban kasar Nijar, Alhaji Mahamadu Issofou, na cikin manyan bakin da suka halarci taron da aka yi a Palais des congrès da ke Yamai.

Ana sa ran mahalarta taron ciki har da wakilan kungiyoyin musulunci da sarakunan gargajiya za su tattauna kan batutuwa da dama.

Ba wannan ne karo na farko da Sarki Muhammdu Sunusi ke kokawa kan yadda ake cin zarafin mata a gidajen aure da kuma yawan sakin su da ake yi barkatai ba.

Sai dai hakan ya sha jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya, inda wasu ke ganin ya yi abun da ya kamata shugabannin su dinga yi, wasu kuma suke ganin wasu kalaman nasa ba su dace ba.

Karanta karin labarai:

Labarai masu alaka