Abubuwa uku da suka sa Buhari neman wa'adi na biyu

Wasu na ganin yana son a sake bashi dama domin ya gyara kura-kurensa. Hakkin mallakar hoto Buhari Sallau facebook
Image caption Wasu na ganin yana son a sake bashi dama domin ya gyara kura-kurensa.

Tun bayan da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da aniyarsa ta sake tsayawa takara domin neman tazarce a zaben 2019 jama'a da dama ke bayyana ra'ayoyinsu game da haka.

Duk da cewa sanarwar ba ta zo wa wasu da mamaki ba, ganin cewa an dade ana hasashen cewa zai tsaya din, amma wasu ba su yi zaton cewa zai yi sanarwar a yanzu ba.

Musamman ganin yadda jam'iyyarsa ta APC ke cikin rudanin shugabanci, da kuma ganin yadda ake ya samun tashe-tashen hankula iri daban-daban a kasar.

Sai dai Hausawa na cewa bikin Magaji ba ya hana na Magajiya.

Ko wadanne dalilai ne suka sa Shugaba Buhari neman tazarce?

Naziru Mikailu ya tattauna da Dr Suleiman Amu Suleiman, masanin siyasa a Jami'ar East Anglia da ke Birtaniya, wanda kuma ya ce bai yi mamakin sanarwar shugaban ba:

1. Hauhawar farashin mai

Hauhawar da farashin mai ya ke yi a baya-bayan nan ya nuna cewa kudi zai ci gaba da shigowa gwamnati domin samun damar yin ayyuka da cika alkawuran da ya dauka sakamakon lokacin da ya samu gwamnatin cikin talauci.

A yanzu akwai kudi a kasar, kuma za a iya yin abubuwa da dama kuma shi ma ya taimaka wurin tara kudin ta hanyar rage wasu abubuwan na barna.

Don haka babu wanda zai so ya bar gwamnati a yanzu, lokacin da ake cikin wadata.

2.Lafiyarsa ta inganta

Shugaban ya samu lafiya sosai fiye da shekarar da ta gabata, lokacin da hankalin wasu da dama ya tashi saboda tabarbarewar lafiyarsa.

Ya shafe wata da watanni a waje yana jinya, kuma ko da ya dawo ya dade kafin ya murmure.

Amma a yanzu ya samu kwarin gwuiwa yana tafiye-tafiye ba tare da wata matsala ba.

A don haka babu shakka wannan ya bashi kwarin gwuiwar sake fitowa takara.

Hakkin mallakar hoto Buhari Sallau facebook
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbanjo

3. Yana son ya gyara kura-kurensa

Ina ganin shi kansa Shugaba Buhari yana ji a zuciyarsa cewa bai taka rawar a-zo-a-gani ba, a shekara ukun da ya shafe a kan karagar mulki.

Yana sane da cewa mutane suna tsammanin ya yi abin da ya fi wanda ya yi, kuma a zahiri bai kai inda jama'a suka yi hasashen cewa zai kai ba ta fuskar ayyuka.

A don haka yana so a sake ba shi dama domin ya gyara kura-kurensa.

Nasarar da ya samu a wannan gwamnatin ba ta kai wacce ya samu ba a lokacin da ya shugabanci Hukumar Kula da Kudaden da ake samu na rarar man fetur, wata PTF, a lokacin mulkin Janar Sani Abacha.

Idan har ya wuce to zai samu damar yin ayyuka ba tare da wani dabaibayi na siyasa ba irin wanda ya makale shi a wannan mulkin nasa ba.

Sai dai ba zan iya cewa zai kai labari ba tukunna domin wannan zai dogara ne kan irin shirin da 'yan adawa musamman na jam'iyyar PDP suka yi.

Sannan kuma da inda ra'ayoyin 'yan Najeriya za su karkata kafin watan Fabrerun 2019 lokacin da jama'a za su sake kada kuri'a.

Labarai masu alaka