Najeriya: An tsawaita wa'adin shugabannin APC

Jam'iyyar ta yanke shawarar ce a wani taron majalisar zartarwar ta kasa da aka yi a birnin Abuja. Hakkin mallakar hoto Buhari sallau Facebook
Image caption Jam'iyyar ta yanke shawarar ce a wani taron majalisar zartarwar ta kasa da aka yi a birnin Abuja.

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tsawaita wa'adin shugabanninta duk kuwa da cewa wa'adin wadansu daga cikinsu ya cika.

Shugabannin za su ci gaba da jan ragamar jam'iyyar ne a matsayin shugabannin rikon kwarya, kafin a gudanar da zabuka.

Jam'iyyar ta yanke shawarar ce a wani taron majalisar zartarwar ta kasa da aka yi a ranar Litinin a birnin Abuja.

Kakakin jam'iyyar Bolaji Abdullahi ya tabbatar wa BBC da cewa ce taron ya amince da a shirya zabubbuka domin zaben shugabanni nan ba da dadewa ba.

Taron majalisar zartarwar ya yi nazari ne a kan rahoton da kwamitin mutane goma wanda gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya jagoranta wanda ya mika mata.

Kwamitin ya ba da shawarar barin shugabannin jam'iyyar a matakin uwar jam'iyyar da kuma jihohi su ci gaba da rike mukamansu.

Malam Bolaji Abdullahi ya ce kundin tsarin mulkin jam'iyyar ne ya amince a sawwake musu sharadin.

Sai dai ya kara da cewa taron ya kuma amince da a shirya manyan tarukan jam'iyyar domin zaben sabbin shugabannin nan ba da dadewa ba.

Ko da yake ba a sanya takamaiman ranar yin tarukan zaben jam'iyyar ba.

To baya ganin matakin da suka dauka ya sabawa bukatar da Shugaba Muhammadu Buhari ya mika wa majalisar na kada a bar shugabannin su yi tazarce?

Sai Malam Bolaji ya ce: "Wannan kuskure ne a ce shawarar da yanke na nuna cewa akwai matsala a jam'iyyar ko kuma ba mu bi shawarar shugaban kasa ba, ina ganin ba haka abin yake ba."

Matakin da jam'iyyar ta dauka dai ba zai hana shugabanin tsayawa domin a sake zabarsu, idan aka zo manyan zabukan jam'iyyar a matakai daban-daban.

Hakkin mallakar hoto Bashi Sallau Facebook
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar APC John Oyegun

A watan da ya gabata ne dai shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar zartarwar da kada ta sabunta wa'adin shugabannin jam'iyyar.

Tun a shekarar 2014 ne dai jam'iyyar ta yi babban zabe, inda ta zabi wadannan shugabannin, duk kuwa da cewa ya kamata a rika yin zabe ne duk bayan shekara biyu.

Sai dai rashin yin taron a bara na ci gaba da janyo cece-kuce a cikin jam'iyyar.

Abin jira a gani shi ne yadda wannan mataki zai shafi rikice-rikicen da jam'iyyar ke fuskanta musamman a tsakanin 'ya'yanta na jihohi a yayin da kasar ke haramar yin wani babban zabe a shekarar 2019.

.

Labarai masu alaka