Uba ya kulle dansa a keji tsawon shekara 20

Wani uba ya kulle dansa a keji tsawon shekara 20 Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani uba ya kulle dansa a keji tsawon shekara 20

'Yan sanda a Japan sun kama wani mutum dan shekara 73 da ake zarginsa da ajiye dansa a wani keji tsawon fiye da shekara 20.

Yoshitane Yamasaki, ya ce ya kulle dan nasa ne wanda yanzu ya ke da shekara 42 a duniya saboda yana fama da lalurar tabin hankali, sannan wani lokacin kuma ya kan yi fada.

Kejin wanda ke da da tsawon mita daya, kuma fadinsa bai wuce mita biyu ba, na cikin wata bukka ne da ke kusa da gidan Mr Yamasaki a birnin Sanda.

Yanzu haka dai dan mutumin wanda ke karkashin kulawar mahukuntan birnin, na fama da durkushewar baya.

Kafafen yada labaran kasar sun ce mahukuntan kasar ne suka ziyarci gidan Mr Yamasaki, bayan da suka samu labarin cewa ya kulle dan nasa.

Masu bincike sun ce sun yi amanna cewa Mr Yamasaki ya fara tsare dan nasa ne tun yana da shekara 16, a lokacin da ya fara nuna alamun kwakwalwarsa ta dan tabu.

Rahotanni sun ce, Mr Yamasaki ya amsa zargin da ake masa, inda ya sanar da mahukunta cewa, yana bai wa dan nasa abinci a kullum, kuma yana barinsa ya yi wanka ko da yaushe.