Buhari zai sake tsayawa takara a 2019, An kubatar da mutum 149 daga hannun BH

Buhari zai sake tsayawa takara a 2019

Shugaban Najeriya Muhamamdu Buhari ya sanar da cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.

Mai taimakawa shugaban na musamman kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

Hakkin mallakar hoto FACEBOOK/BUHARI SALLAU

An kubatar da mutum 149 daga hannun BH

Rundunar sojin Najeriya ta ce sojojinta sun kubatar da mutum 149 daga hannun mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar.

Sojojin sun kashe mayaka Boko Haram uku ya yin da suka kama biyar a farmakin da sojojin suka kai a karshen mako.

Image caption Sojojin sun kubatar da mata 54 da kuma yara 95

An hana 'yan agajin kungiyar Izala sa inifom

Rundunar 'yan sandan jihar Maradi a Jamhuriyar Niger ta nemi da 'yan agajin kungiyar Izalatul Bid'a Wa Ikamatussunnah na jihar da su dakata da sanya kayan sarki na agaji har zuwa wani dan lokaci.

Sulaiman Hashimu shugaban 'yan agajin a jihar Maradi ya shaida wa BBC cewa sun samu sako ne daga 'yan sandan jihar, inda aka ce an dakatar da su daga sanya kayan inifom na agaji.

Hakkin mallakar hoto JIBWIS Nigeria

Uba ya kulle dansa a keji tsawon shekara 20

'Yan sanda a Japan sun kama wani mutum dan shekara 73 da ake zarginsa da ajiye dansa a wani keji tsawon fiye da shekara 20.

Yoshitane Yamasaki, ya ce ya kulle dan nasa ne wanda yanzu ya ke da shekara 42 a duniya saboda yana fama da lalurar tabin hankali, sannan wani lokacin kuma ya kan yi fada.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani uba ya kulle dansa a keji tsawon shekara 20

Buhari ya fara ziyarar aiki a Burtaniya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya fara wata ziyarar aiki a Burtaniya, inda ake sa ran zai gana da Firayi ministar kasar Theresa May da shugannnin wasu kamfanonin hakar mai.

Shugaban ya bar Abuja zuwa birnin Landan a ranar Litinin.

Hakkin mallakar hoto Facebook/Buhar Sallau

An tsawaita wa'adin shugabannin APC

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tsawaita wa'adin shugabanninta duk kuwa da cewa wa'adin wadansu daga cikinsu ya cika.

Shugabannin za su ci gaba da jan ragamar jam'iyyar ne a matsayin shugabannin rikon kwarya, kafin a gudanar da zabuka.

Hakkin mallakar hoto Bashi Sallau Facebook
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari da shugaban jam'iyyar APC John Oyegun

Karanta karin wasu labaran

Domin samun karin bayani da kuma tofa albarkacin bakinku a kan wadannan labaran, sai ku garzaya shafinmu na BBC Hausa Facebook.

Labarai masu alaka