Mutum 2,000 sun mutu a rikicin manoma da makiyaya

An kiyasta cewa an yi asarar dukiya ta miliyoyin naira da kuma dubban rayuka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An kiyasta cewa an yi asarar dukiya ta miliyoyin naira da kuma dubban rayuka

Wata kungiyar kare hakkin dan Adam a Najeriya ta ce fiye da mutum 2,000 ne suka mutu sakamakon rikicin manoma da makiyaya a fadin kasar.

A wani rahoto da kungiyar mai suna The Coalition on Conflict Resolution and Human Rights in Nigeria ta fitar ranar Litinin ta ce, dubban 'yan kasar sun kuma rasa muhallansu sakamakon rikicin.

A cewar kungiyar, an samu adadin mutanen ne daga bin diddigin da take yi a rikice-rikicen da ake ta samu tsakanain manoma da makiyaya a fadin kasar.

Kungiyar ta ce rikicin ya fi shafar jihohin da ke yankin arewa ta tsakiyar Najeriyar ne da suka hada da Binuwai da Taraba da Filato da Kogi da kuma Nassarawa, abun da ya sa hukumomi suka sanya dokar ta baci a wasu yankunan.

Rahotanni sun nuna cewa baya ga rikicin manoma da makiyaya, 'yan bindiga na kuma amfani da damar wajen tayar da zaune tsaye don kashe mutane da sace-sace a al'ummu da dama.

A yanzu haka dai runsunar soji ta aike da dakaru zuwa wasu yankunan da abun ya shafa an kuma kama wasu da dama da ake zargi da hannu a lamarin, amma har yanzu ana ci gaba da kai hare-hare wasu kauyukan da ke cikin surkuki.

Rikicin manoma da makiyaya

Rikicin manoma da makiyaya dai a Najeriya ya yi sanadin asarar rayuka daga dukkan bangarorin biyu, al'amarin da ya jawo hankalin kusan daukacin 'yan Najeriya.

Rikicin ya fi kamari ne a jihohin Filato da Benue da Taraba da Nassarawa da Kaduna.

Hakkin mallakar hoto AFP

A baya gwamnatin tarayya ta yi kira ga gwamnonin jihohin da lamarin ya shafa su samar da wuraren kiwo.

Sai dai gwamnonin sun yi fatali da wannan kira, suna masu cewa ba su da isassun filayen da za su bayar domin kiwo.

Amma a watan Fabrairu Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya gayyaci Fulani makiyaya su koma jiharsa domin gudanar da kiyo ba tare da samun matsala ba.

Labarai masu alaka