Gobara ta kashe mutum 8 a sansanin 'yan gudun hijira a Borno

Rann Hakkin mallakar hoto EPA

Rahotanni daga garin Rann da ke karamar hukumar Kala Balge a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, sun ce a kalla mutum takwas sun rasa rayukansu yayin da wasu fiye da 20 kuma suka jikkata sakamon wata gobara.

Wutar, wadda ta fara tashi a sansanin 'yan gudun hijira da ke garin a ranar Juma'ar da ta gabata, ta kona Tantuna 3,600 kuma ta shafe kusan kwana biyar tana ci.

Wani mazaunin sansanin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa BBC cewa, "Wutar ta fara ne tun daga ranar Juma'a har kawo ranar Litinin, kuma wutar dafa abinci ce ta haddasa ta.

"Wutar ta kuma kona tantuna 3,600, kuma mun sanar da gwamnati batun wutar amma ba a kula da mu ba, sai dai sojoji ne suke taimaka mana, yanzu haka yara kanana ma sun fara mutuwa saboda yunwa da zafi."

To sai dai kuma a nata bangaren gwamnatin jihar ta bakin shugaban kwamitin kula da ayyuykan jin kai na jihar, Injiniya Satomi Ahamad, ya ce ko shakka babu gwamnati ta san da wannan lamari, amma kuma tana iya bakin kokarinta wajen ganin an taimakawa mazauna garin.

Injinya Satomi ya ce, hanyar zuwa garin ba ta da kyau, wannan dalili na daga cikin dalilan da ya sa ba a kai musu dauki a kan lokaci ba.

To amma ya ce yanzu gwamnatin jihar ta ware wasu makudan kudade domin gyaran hanyar.

Injiniya Satome ya kuma ce: "A yanzu haka da nake magana, an tanadi kayayyakin abinci da kuma wadanda ba na abinci ba, kamar su bargo da tabarmai wanda an kai na farko.

"Kuma a ranar Litinin an kai musu abinci wanda za a raba na wata biyu, kuma a gaba ma za a raba na wasu wata biyun," in ji Satomi.

Karin bayani

Ba wannan ne karo na farko da iftila'i ke afkawa sansanin 'yan gudun hijira a jihar Rann da ke Kale Balge ba.

Ko a farkon watan Maris din da ya wuce ma, wasu ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya uku sun rasa rayukansu a yayin da masu tayar da kayar baya suka kai hari wani sansanin sojoji da ke garin.

Kazalika a watan Janairun 2017 mutum 115 sun mutu a harin da wani jirgin saman yaki na Najeriya ya kai bisa kuskure kan sansanin 'yan gudun hijira dake garin.

Labarai masu alaka