Ana yawan kashe 'yan Najeriya a Landan - Abike Dabiri

Landan

Jami'ai a Najeriya sun nuna damuwa a kan kisan 'yan asalin kasar da ke karuwa a London.

Babbar mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin waje da 'yan Najeriya mazauna ketare, Abike Dabiri Erewa ta ce an kashe 'yan kasar da dama a cikin watanni uku na farkon wannan shekara.

A makon jiya ne dai Miss Dabiri ta rubuta wasikar koke ga ofishin jakadancin Burtaniya da ke Abuja.

Sai dai Burtaniyar ta ce tana daukar matakai a kan lamarin.

Miss Dabiri ta ce kimanin bakaken fata 50 aka kashe a birnin na London a 'yan watannin da suka wuce.

Inda ta ce abin da ke tayar da hankali shi ne 'yan asalin Najeriya kimanin goma ne aka harbe ko kuma aka dabawa wuka tun watan Janairu na wannan shekarar.

Kuma mafiya yawansu matasa ne masu shekaru 18 zuwa 26.

Mai taimaka mata ta fuskar yada labarai, AbdurRahman Balogun, ya shaida wa BBC cewa: "A makon da ya gabata an rubuta wasikar koke daga ofishinta zuwa ga ofishin jakadancin Burtaniya da ke Najeriya a kan kisan Abraham Badru daga ga wani dan majalisa a Najeriya."

Inda ya kara da cewa ko a bara ma sai da ofishin nata ya aike da irin wannan wasikar, amma jakadan Burtaniya, Paul Arkwright mika jaje ga iyalan wadanda abin ya shafa.

Ya kuma ce kasarsa na bincike a kan lamarin kuma har an kama wasu da ake zargi da hannu a kashe-kashen.

Sai dai Miss Dabiri ta bukaci 'yan asalin Najeriya su dinga taka tsantsa tare da nuna halayya ta gari a kasashen da suke zaune, su kuma zama masu bin doka da oda.

Wasu alkaluma da aka fitar ya nuna cewa 'yan sandan birnin London na bincike a kan zargin kisa 15 da aka aikata da wuka a watannin Fabrairu da Maris din da suka gabata, adadin da ya zarta kisa 11 da ake zargin an aikata da wuka a birnin New York na Amurka.

Labarai masu alaka