An kama mai hada wa Boko Haram bama-bamai

Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta na samun nasarar fatattakar 'yan Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar sojin Nigeria ta ce dakarunta na samun nasarar fatattakar 'yan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kama wani mutum da ya shahara wajen hada bama-bamai ga mayakan kungiyar Boko Haram.

Rundunar ta ce an kama Adamu Hassan ne da ake yi wa lakabi da suna 'Baale' a garin Kaltungo na jihar Gombe da ke shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar Operation Lafiya Dole Kanar Onyema Nwachukwu, ya ce an kama mutumin ne a wani samame da jami'an hukumar tsaro ta farin kaya suka kai.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ambato Kanar Nwachukwu na cewa dakarun sojin kasar sun kashe mayakan Boko Haram uku a bata kashi da suka yi a tsaunukan Bokko Hilde da ke kan hanyar Ngoshe zuwa Pulka a jihar Borno.

Labarai masu alaka