Kun san fina-finan Bollywood da suka fi fice a 2018?

Padmavati

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jaruman da suka fito a fim din sun hadar da Deepika Padukone da Ranvir Singh da kuma Shahid Kapoor

An saki fim din Padamavati a ranar 25 ga watan Janairun 2018. Sanjay Leela Bhansali ne ya bayar da umarninsa.

Fim ne da ya kunshi labarin wata kyakkyawar sarauniya daga bangaren mabiya addinin Hindu wadda aka taba yi a karni na 14, tare da wani sarki musulmi.

Fim ne da ya yi fice kwarai da gaske a shekarar domin ya kawo kudi kusan dala miliyan 90.

Jaruman da suka fito a fim din sun hadar da Deepika Padukone da Ranvir Singh da kuma Shahid Kapoor.

Pad Man

Hakkin mallakar hoto SONY PICTURES
Image caption Jarumi Akshay Kumar da Sonam Kapoor ne suka fito a ciki

An saki Fim din Pad Man a ranar 9 ga watan Fabrairun 2018. Fim ne wanda Twinkle Khanna ta shirya shi, R. Balki kuma ya bayar da umarninsa.

Fim ne da ya kunshi barkwanci kuma an yi shi ne da nufin wayar da kan mutane a kan su dai na kyamatar mata idan suna jinin al'ada.

An kuma yi nuni da yadda za a rinka samar da auduga mai sauki domin matan da ba su da halin siyan mai tsada ta yadda za a daina amfani da kunzugu idan mace na al'ada.

Wannan fim din ma ya yi fice kwarai da gaske saboda yadda aka gina labarin. Jarumi Akshay Kumar da Sonam Kapoor ne suka fito a ciki.

Hichki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Fin din Hichki ya samu karbuwa a wajen jama'a sosai

Hitchki, fim ne wanda Maneesh Sharma ya shiya shi, Sidharth P Malhotra kuma ya bayar da umarninsa.

An sake shi a ranar 23 ga watan Maris na bana. Jaruma Rani Mukherjee ce ta fito a cikin fim din.

Fim din ya kunshi labarin wata mata mai fama da larurar Tourette's (wata larura da kan shafi laka wadda alamominta su ne motsin wasu sassan jiki da fitar sauti ba da niyya ba).

Bayan ta yi ta cin karo da rashin nasara a yunkurinta na neman aiki, sai ta samu aiki a matsayin malama a wata makarantar 'ya'yan masu hannu da shuni.

Ba ta jima ba ta fara gwagwarmayar nusar da dalibanta marasa ji don su gane irin baiwar da Allah ya yi musu. Shi ma wannan fim din ya samu karbuwa a wajen jama'a sosai.

Baaghi 2

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Fim din Baaghi 2 ya mayar da hankali ne kan fada

Fim ne na fada sosai wanda jarumi Tiger Shroff da Disha Patani suka fito a ciki. Ahmed Khan shi ya bayar da umarninsa.

An saki fim din a ranar 30 ga watan Maris 2018. Fim din ya samu karbuwa sosai musamman a kasar India, ya kuma kawo kudi.

Baaghi labarin wani gwarzon jarumi wanda ya yi tsaiwar daka don kalubalantar masu safarar kwayoyi da wasu 'yan gani-kashe-nin siyasa 'yan kasar Rasha, don kubutar da tsohuwar budurwarsa da aka yi garkuwa da ita a birnin Goa na kasar India.

October

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption October ba labarin soyayya ba ne, amma labari ne game da soyayya.

Fim ne da aka sake shi a ranar 13 ga watan Afrilun 2018. Shoojit Sircar ne ya bayar da umarninsa.

Varun Dhawan da sabuwar yarinya Banita Sandhu suka fito a ciki. Labari ne na Dan (Varun Dhawan) da ke tafiyar da rayuwarsa kamar kowane matashi dan shekara 21 .

Yana tare da abokansa da abokan sanin makamar aiki a otel din da yake aiki, wadanda ke neman sanin halin da sauran ke ciki a kodayaushe.

Shiuli (Banita Sandhu) na daya daga cikin masu neman sanin makamar aiki a otel din, wadda a lokuta da yawa ke fuskantar halin Dan na fada wa rayuwa gaba-gadi ba tare da tunani ba.

Rayuwarsu ta ci gaba a haka har lokacin da wani sauyi ya zo musu kwatsam, sauyin da ya rikita rayuwarsu, ya saka su a cikin wani halin da masu shekara 21 basu taba fuskanta ba.

Wannan shakuwar da suka yi ta rika sauyawa har ta kai su ga wata irin soyayya da ba kasafai ake ganin irinta ba.

October ba labarin soyayya ba ne, amma labari ne game da soyayya.

Labarai masu alaka